Cristiano Ronaldo ya yi godiya bayan Edinson Cavani ya ci girma, ya damka masa lamba 7

Cristiano Ronaldo ya yi godiya bayan Edinson Cavani ya ci girma, ya damka masa lamba 7

  • Cristiano Ronaldo ne zai goya #7 wannan shekarar a Manchester United
  • Kungiyar ta tabbatar da cewa Edinson Cavani ya yarda ya koma goya #21
  • Ronaldo ya karbi lambar da kowa ya san shi da ita shekarun baya a Ingila

England – Kungiyar kwallon kafan Manchester United ta tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo zai sa riga mai lamba 7 ne a kakar shekarar nan a Old Trafford.

‘Dan wasan na kasar Portugal ya goya wannan riga a lokacin da ya buga wa Manchester United kwallo a karon farko tsakanin shekarar 2003 da kuma 2009.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa Ronaldo ya karbi rigarsa.

7 tana da tarihi a Old Trafford

7 ta na da dogon tarihi a Manchester United domin irinsu George Best, Bryan Robson, Eric Cantona da kuma David Beckham ne suka goya wannan lamba.

Kara karanta wannan

Tsohon ‘Dan wasan Real Madrid ya bada labarin wani fadan Ronaldo da Jose Mourinho

Cristiano Ronaldo ya gaji tsohon ‘dan wasan Ingila David Beckham a lokacin da ya zo Ingila. Bayan shekaru bakwai ya bi sahun Beckham, ya koma Madrid.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ronaldo ya gaji rigar mai tarihi ne daga Edinson Cavani wanda ya buga wasan da Manchester ta samu nasara a makon jiya a gidan Wolverhampton Wanderers

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo zai goya #7 Hoto: www.manutd.com
Asali: UGC

Wace lamba Cavani zai goya?

Cavani zai koma goya lamba 21 da ya saba goya wa yayin da yake buga wa kasar Uruguay wasa.

Kungiyar kwallon tace shi kuma ‘dan wasan kasar Uruguay, Edinson Cavani ya nuna dattaku, ya bar sabon sayayyan ya sa wannan riga da kowa ya san shi da ita.

Tashin Daniel James daga Manchester zuwa Leeds United ta bada dama Cavani ya karbi 21. Ronaldo ya nuna ya ji dadin halin girman da Cavani ya nuna masa.

Kara karanta wannan

Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi da kasar Portugal a Duniyar wasan kwallon kafa

Ronaldo yace bai taba tsammanin rigarsa za ta dawo ba. Ga duk mai bukatar sayen rigar Tauraron, zai iya tuntubar shagon United Direct a kafar yanar gizo.

Ronaldo bai da tamka

Kun ji cewa Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu a wasan Portugal da Ireland. Hakan ya sa ya kafa sabon tarihi da kasar Portugal a Duniyar wasan kwallon kafa.

Tsohon ‘dan wasan na Juvenuts da Real Madrid shi ne ‘dan wasan da ya fi kwallaye a gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng