Lauya ya janye hannu daga lamarin Abduljabbar Kabara, ya nemi afuwar KaribulLah da Musulmai

Lauya ya janye hannu daga lamarin Abduljabbar Kabara, ya nemi afuwar KaribulLah da Musulmai

  • Barista Rabiu Abdullahi Shu’aibu ya nemi al’ummar musulmai su yafe masa
  • Lauyan ya bayyana haka bayan sun janye kansu daga karar babban malamin
  • Rabiu Abdullahi Shu’aibu yace babu mamaki ya saba wa musulmai da aikinsa

Kano - Rabiu Abdullahi Shu’aibu wanda yana cikin manyan lauyoyin da suka rika tsaya wa Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi magana bayan janye hannunsa.

A makon da ya gabata ne aka ji Barista Rabiu Abdullahi Shu’aibu ya fitar da wani faifan sakon sauti a shafin Facebook wanda ya shigo hannun Legit.ng Hausa.

Za a ji lauyan yana fada wa wani Alhaji cewa sha’anin shehin malamin ya zo kansu, duk da irin kokarin da suka rika yi a da na ganin sun kare shi a gaban Alkali.

Kara karanta wannan

Yadda rigima ta kaure tsakanin Abduljabbar Kabara da Lauyoyinsa har Alkali ya daga shari’a

Rabiu Abdullahi Shu’aibu ya nemi al’ummar musulmi su yafe masa laifinsa, musamman Khalifan darikar Qadriyyah na Afrika, Sheikh KaribulLahi Nasiru Kabara.

Baristan yake cewa ya san ya yi wa Sheikh KaribulLahi Nasiru Kabara wajen kare ‘danuwansa.

Kamar yadda muka ji, lauyan bai bayyana laifin da ya yi wa al’umma ba, amma yace babu mamaki ya yi wa wasu ba daidai ba da bakinsa ko ta hanyar aikinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abduljabbar Kabara
Shehin malami Abduljabbar Kabara Hoto: www.dw.com
Asali: UGC

A yafe mani - Rabiu Abdullahi Shu’aibu

“Mu ma wannan mutumi ya zo kanmu bayan duk abin da muka yi masa. Allah ya sawake.”
“Duk wadannan abubuwa da suka faru, abin da na ce shi ne, na farko in nemi afuwar duk wani mutum da na cutar ko da harshe na, ko da aikina a kan Abduljabbar.”

Lauya ya yi wa Khalifa KaribulLahi laifi?

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Mun cafke mutum fiye da 100 da ke ba ‘Yan bindiga bayanai a Zamfara - Matawalle

“Musamman ‘danuwansa, Khalifa KaribulLahi (Nasiru Kabara). Ya kamata in nemi afuwarsa, in nemi yafiyarsa.”
“Kuma Alhaji idan akwai wata hanya da za ka iya isar da wannan sakon na wa, tun da na san alakarka da shi, don Allah ina bukatar a isan mani da sako.”
“Ina so a fada masa cewa ni Barista Rabiu Abdullahi Shu’aibu, ina neman afuwarsa idan nayi masa wani abu ko da baki na, ko da aiki na a kan Abduljabbar.”
“Ni dai a tunani na, na san na yi (laifi). Zai iya yiwu shi kuma bai san na yi ba. Amma ina neman afuwa domin akwai abubuwan da ‘dan Adam ba ya gane wa, sai yau da gobe yake sa shi gane.”

A cewar lauyan yau da gobe ta sa ya gane gaskiya domin an ce duk wanda ranaku ba su amfanar da shi ba, abin da mai wa’azi ya yini yana fada ba zai amfane shi ba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumin Kannywood, Ahmad Tage rasuwa

Meya hada Sheikh Abduljabbar Kabara rigima da lauyoyinsa?

A makon jiya rigima ta nemi ta kaure tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da Lauyoyin sa a kotu. Lauyoyin da suka tsaya wa malamin suna zarginsa da yi masu sharri.

Shehin malamin ya zargi lauyoyin da yaudararsa, da kuma damfarar matarsa. Amma lauyoyin da suka tsaya wa malamin sunce duk abubuwan da yake ta fada karya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel