Daga shigarsa APC, an ga fostar Femi Fani-Kayode yana neman Mataimakin Shugaban kasa

Daga shigarsa APC, an ga fostar Femi Fani-Kayode yana neman Mataimakin Shugaban kasa

  • Wasu hotunan sun nuna Femi Fani-Kayode yana neman Mataimakin Shugaban kasa
  • Fastocin sun nuna sabon shigan na APC zai tsaya takara ne tare da Yahaya Bello
  • Kungiyar Magoya bayan Bello tace ba ta san da zaman fastocin da ke ta yawo ba

Hotunan neman takarar gwamna Yahaya Bello da tsohon Ministan harkokin jiragen sama, Femi Fani-Kayode suna yawo a kafofin sadarwa na zamani.

A ranar Lahadi, jaridar Independent ta kawo rahoto cewa wadannan fastoci suna dauke da taken “Yahaya and Femi 2023” tare da tambarin jam’iyyar APC.

Fastocin sun nuna Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello yana neman kujerar shugaban kasa, yayin da Femi Fani-Kayode ya tsaya a matsayin mataimakinsa.

Nigeria youths Awareness Group mai goyon bayan takarar Yahaya Bello ta fito tayi magana, inda ta nesanta kanta daga fastocin da suka fara yawo a kasar.

Kara karanta wannan

Wajibi Yan Najeriya Su Taimaki FG Wajen Yaki da Matsalar Tsaro a Najeriya, Sanata Lawan

Jaridar Sun tace shugaban Nigeria youths Awareness Group for Yahaya Bello, 2023 watau Alhaji Salihu Magaji yace sam ba su san da wannan maganar ba.

Femi Fani-Kayode yana neman Mataimakin Shugaban kasa
Fostar Yahaya Bello da Fani-Kayode Hoto: www.reubenabati.com.ng
Asali: UGC

Ba da hannunmu aka yi ba - Masoya

Alhaji Salihu Magaji yace ba su da masaniyar cewa gwamna Bello ya hada-kai da wani ‘dan siyasa da nufin ya tsaya masa takarar mataimakin shugaban kasa.

“An jawo hankalinmu kan wasu fastoci da ke yawo dauke da Yahaya Bello da Femi Fani Kayode a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa.”
“An fito da hotunan takarar na 2023 da sunan mu, ana yada su a kafofin sadarwan zamani.”
“Muna so mu bayyana cewa Gwamna Bello bai da masaniyar wannan, kuma babu ruwan kungiyar ko wani mutum da wadannan fastoci.”

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Salihu Magaji yake cewa Bello ba zai yi azarbabi ba, domin sai bayan zaben fitar da gwani ne sannan ake dauko ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Sauya-shekar FFK ta yi farin jini?

A makon jiya ne aka tabbatar da cewa tsohon Ministan ya koma APC. Sai dai wasu jiga-jigan APC da PDP duk sun la’anci sauya-shekar da Fani-Kayode ya yi.

Irinsu Reno Omokri sun ce PDP ta samu wanda ya fi Femi Fani-Kayode washegarin komawarsa Jam’iyyar APC, ganin cewa Sanata Shehu Sani ya shiga PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel