Jerin Gwamnoni da yan siyasa 26 da sukayi takakkiya zuwa Landan don gaida Tinubu
A watan Yuli an kwantar da tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, a wani asibitin waje, inda aka yi masa aikin Tiyata a gwiwa.
Da farko mai magana da yawun bakin ‘dan siyasar, Tunde Rahman, ya kartaya wannan batu, yace Tinubu ya na kasar waje, amma ba jinya yake yi ba.
Amma daga baya da Buhari ya ziyarcesa, ya bayyana cewa lallai an yi masa tiyata.
Tun daga lokacin, kimanin yan siyasa 30 sun yi takakkiya daga Najeriya zuwa Landan don masa ziyarar gaisuwa.
Ga jerin yan siyasan da suka ziyarci Asiwaju Bola Tinubu a Landan:
1. Shugaba Muhammadu Buhari
2. Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos
3. Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo
4. Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti
5. Gwamna Umar Ganduje na Kano
6. Femi Gbajabiamila - Kakakin Majalisa
7. Sanata Ibikunle Amosun
8. Tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima
9. Usman Zanna, Dan majalisar wakilai
10. Obafemi Hamzat - Mataimakin Gwamnan Legas
11. Tayo Ayinde - Shugaban ma'aikatan gwamnan Legas
12. Gboyega Soyannwo - Mataimakin Shugaban ma'aikatan gwamnan Legas
13. Tokunbo Wahab - Bababn hadimin Sanwo-Olu kan ilimi
14. Muiz Banire - Babban jigon APC
15. Mudashiru Obasa - Kakakin majalisar Legas
16. Temitope Adewale - Dan majalisar Legas
17. Nureni Akinsanya - Dan majalisar Legas
18. Sylvester Ogunkelu - Dan majalisar Legas
19. Sanata Adetokunbo Abiru (Lagos East)
20. Sanata Opeyemi Bamidele (Ekiti Central)
21. Sanata Adeola Solomon (Lagos West)
22. Sanata Adelere Oriolowo (Osun West)
23. Sanata Mohammed Sanni (Niger East)
24. Sanata Olasoju - Chairman, Isolo LCDA
25. Adekunle Akanbi
26. Wasiu Ayinde, dss
Asali: Legit.ng