Ina da kudi, Mijin aure kawai nake nema: Budurwa ta fito titi tallar kanta

Ina da kudi, Mijin aure kawai nake nema: Budurwa ta fito titi tallar kanta

  • Wani abin mamaki, wata budurwa ta shiga titi tana neman Mijin aure
  • Budurwar yar kasar Tanzania tace yanzu haka akwai zobe biyu hannunta, na ta da na mijin
  • Tace duk namijin da ya amince kada ya damu, akwai kudi hannunta

Wata mata mai neman mijin aure ta shiga gari rike da allo a garin Buza, Dar es Salaam tana bayyana irin namijin da take bukata don aure.

A wani bidiyon Youtube, an ga matar da Allo mai rubutun cewa:

"Ina neman Miji mai shekaru 20 zuwa 70."

Wa zai biya Sadaki?

Yayinda take magana da wani dan jarida a kasar, budurwar tace tana da budurcinta kuma za ta biya kudin sadaki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Makashin Ɗan Sanata Na'Allah: Buhunan Shinkafa 23 Na Siya Da Kason Kuɗi Na

A cewarta:

"Har zobunan aure ina da su. Zan biya kudin sadaki kuma har kayan da zai sa ranar aure zan bashi."
"Ni Kirista ce amma ban da matsala zan iya Musulunta muddin mutumin mai tsoron Allah ne."

Ina da kudi, Mijin aure kawai nake nema: Budurwa ta fito titi tallar kanta
Ina da kudi, Mijin aure kawai nake nema: Budurwa ta fito titi tallar kanta Hoto: Simulizi Na Sauti
Asali: UGC

Ina da kudi

Ta kara da cewa tana da isassun kudi kawai tana neman mijin da zai so ta ne.

"Ina da kudi, ban son takurawa wani namiji."
"Na hadu da maza da yawa da suke son su gana da ni a dakin Otal amma naki."

Kalli bidiyon:

Dan siyasa a kasar Tanzania ya angwance da kyakkyawar mata

Shahrarren dan siyasa a kasar Tanzania, Petro Magoti, ya saki hotunan daurin aurensa da kyakkyawar budurwa bayan cika alkawarin da yayi mata ranar 29 ga Mayu, 2021.

Hotunan daurin auren dan siyasan sun cika kafafen ra'ayi da sada zumunta kuma mutane na tofa albarkatun bakinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel