Bayan Buhari ya ziyarci jihar Imo, Mai magana da yawun bakin Jam’iyyar PDP ya sauya-sheka

Bayan Buhari ya ziyarci jihar Imo, Mai magana da yawun bakin Jam’iyyar PDP ya sauya-sheka

  • Ogubundu Nwadike ya koma APC a Imo, ya yi watsi da jam’iyyar hamayya
  • Kafin yanzu Nwadike ne babban sakataren yada labarai na PDP a jihar Imo
  • Ambrose Nwaogwugwu ya bada wannan sanarwa ta shafinsa na Facebook

Imo - Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na jihar Imo, Ogubundu Nwadike, ya sauya-sheka zuwa APC mai mulki.

Daya daga cikin manyan jiga-jigan APC a jihar Imo, Mista Ambrose Nwaogwugwu, ya bada sanarwar fice war Ogubundu Nwadike daga jam’iyyar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ambrose Nwaogwugwu yana cewa Ogubundu Nwadike ya rubuta takardar murabus, ya yi watsi da jam’iyyar hamayyar.

‘Yan jarida sun yi yunkurin tuntubar Ogubundu Nwadike a waya amma abin ya faskara. Nwadike wanda shi ne kakakin PDP a Imo ya ki daukar wayarsa.

Kara karanta wannan

2023: Arewa za ta tashi da tikitin shugaban kasa a PDP, Yarbawa da Shugaban Jam'iyya

Rahotanni sun tabbatar da cewa an hangi Mista Ogubundu Nwadike a sakatariyar jam’iyyar APC ta Imo yana gode wa shugabannin APC da suka karbe shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai magana da yawun bakin Jam’iyyar PDP
Tsohon kakakin PDP na Imo @Ambrose Nwaogwugwu.
Asali: Facebook

Nwadike ya bar PDP - Ambrose Nwaogwugwu

Da yake magana a Facebook, Nwaogwugwu ya tabbatar da sauyin-shekar jami'in na jam’iyyar PDP.

“Na yi aiki da Ogubundu Nwadike a lokacin da nake Darekta-Janar na jam’iyya. Abin farin ciki ne ganin ana yi masa maraba a cikin jam’iyyar APC.”
“Dole in jinjina wa Nwadike kan karfin-halin da ya yi, ya yi fatali da lemar da ta kece, wanda ta tabbatar da kanta a matsayin makiyiyar jihar Imo.”
“Duk wani ‘dan kwarai mai kishi a Imo ba zai iya cigaba da zama da wannan jam’iyya da ta rantse sai ta kai jihar kasa saboda tsabagen son-kan ta ba.”

Kara karanta wannan

Da duminsa: An hallaka Shugaban yan ta'addan ISWAP, AlBarnawy

Nwaogwugwu yace babu wani mai kishi da zai ga irin ayyukan da gwamna Hope Uzodimma yake yi, kuma ya zabi ya cigaba da yi wa gwamnatinsa adawa.

Jam’iyyar PDP ba tace komai ba har yanzu, amma Nwaogwugwu yace wasu za su cigaba da shigo wa APC.

Lissafin 2023

Dazu kun ji cewa Yarbawan PDP suna ganin an yi masu bukulu a 2017. Wannan karo Prince Oyinlola zai gwabza da su Bode George wajen zama Shugaban PDP.

Alamu na nuna cewa yankin Arewa za a bari su fito da 'dan takarar shugaban kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel