Ibo sun fito da Okonjo-Iweala, Okorocha, Obi da wasu 15 cikin wadanda za su iya rike Najeriya

Ibo sun fito da Okonjo-Iweala, Okorocha, Obi da wasu 15 cikin wadanda za su iya rike Najeriya

  • Umunna Lekki Association ta kawo ‘ya ‘yan ta da za su iya takara a 2023
  • Kungiyar ta fito da ‘yan siyasa daga duka jihohin dake Kudu maso gabas
  • Orji Uzoh Kalu, Peter Obi, Ogbonna Onu da David Umahi sun samu shiga

Bayan kiraye-kirayen mika mulki ga kudu maso gabashin Najeriya, wasu matasan kasar Ibo sun fito da wadanda suke ganin za su iya neman takara a 2023.

Kungiyar Umunna Lekki Association ta ‘yan kasuwa da mazauna Ibo da ke Lekki, Ikoyi, Banana Island, VGV da VI a garin Legas sun fara fito da muradinsu.

Jaridar Daily Trust tace wannan kungiya ta shirya ganin Ibo ya zama shugaban kasa a zaben 2023.

Umunna Lekki Association ta bibiyi jihohin kudu maso gabashin Najeriya biyar, ta zakulo wasu fitattun mutane da za su iya rike tutar takarar shugaban kasa

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okonjo-Iweala, Peter Obi da wasu 'yan siyasa 16 na kudu maso gabas da aka nemi suyi takara

Su wanene wadanda aka fito da su?

Daga cikin wadanda aka fito da su daga Abia akwai shugabar WTO, Dr. Ngozi Okonji Iweala, Sanata Enyinnaya Abaribe, tsohon Gwamna Orji Uzoh Kalu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Okonjo-Iweala a Aso Villa
Buhari da Dr. Nkonjo Iweala Hoto: www.radionigeria.gov.ng
Asali: UGC

A Anambra akwai tsohon gwamna Peter Obi, Charles Udeogaranya, Ben Obi da Henry Okolie-Aboh.

Wadanda aka zakulo daga Ebonyi sune gwamna Dave Umahi, Ministan kimiyya da fasaha Ogbonnaya Onuh da tsohon SGF, Sanata Anyim Pius Anyim.

A Enugu an zakulo Geoffrey Onyema, Farfesa Barth Nnaji, Nnia John Nwodo Jnr da tsohon shugaban mataimakin majalisar dattawa, Ike Ekweremadu.

Daga jihar Imo akwai Emeka Ihedioha, Rochas Okorocha, Kema Chikwe Da Humphrey Anumudu.

Jaridar tace shugaban wannan kungiya, Ikem Umeh-Ezeoke, ya fitar da jawabi, ya zakulo wadannan fitattun mutane daga jam’iyyun APC da na PDP.

Yamutsi a APC ta Taraba

Kara karanta wannan

Jiga-jigan APC sama da 30 suna harin kujerar Ministan wutan lantarki da aka tsige

A jiya ne aka ji labari jiga-jigan APC sama da 30 a jihar Taraba suna harin kujerar Ministan wutan lantarki, Saleh Mamman da aka tsige daga ofis kwanaki.

Shugaban jam’iyyar na Taraba yace mutane har 32 suke harin kujerar Ministan. Daga ciki akwai Garba Umar, Sani Danladi da su Sanata Yusuf Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng