Da duminsa: Jarumin Kannywood, Yusuf Barau, ya riga mu gidan gaskiya

Da duminsa: Jarumin Kannywood, Yusuf Barau, ya riga mu gidan gaskiya

  • Allah ya yi wa tsoho kuma fitaccen jarumin Kanywood, Yusuf Barau rasuwa
  • Jarumi Lawan Ahmad ya wallafa hoton jarumin tare da masa fatan rahamar Allah
  • Bayan nan, ya kara da yi wa iyalansa da abokan arzikinsa fatan jure babban rashin

Kano - Daga Allah mu ke, gare shi za mu koma. Allah ya yi wa jarumin Kannywood, Yusuf Barau rasuwa.

Kamar yadda Legit.ng ta gano a shafin jarumi Lawan Ahmad, tsohon jarumin ya rasu inda ya bar iyalinsa.

Bayan bayyana rasuwar, Lawan Ahmad ya kara da yi wa jarumin fatan rahamar Allah tare da juriya ga iyalansa da abokan arzikinsa.

Da duminsa: Jarumin Kannywood, Yusuf Barau, ya riga mu gidan gaskiya
Da duminsa: Jarumin Kannywood, Yusuf Barau, ya riga mu gidan gaskiya. Hoto daga @lawanahmad
Asali: Instagram

Har a lokacin rubuta wannan rahoton, babu cikakken bayani kan rasuwar tsohon jarumin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamnatin Dubai ta alanta neman yan Najeriya 6 ruwa a jallo, jerin sunayesu

Karin bayani na nan zuwa...

Asali: Legit.ng

Online view pixel