Da duminsa: Gwamnatin Dubai ta alanta neman yan Najeriya 6 ruwa a jallo, jerin sunayensu
1 - tsawon mintuna
- Akwai sunan yan Najeriya shida cikin jerin yan ta'addan da UAE ke nema
- Sunayen sun nuna cewa akwai alamun dukkansu yan Arewa ne
- Har yanzu, yan Najeriya ba sa iya zuwa kasar UAE tun bayan da kasar ta kakaba takunkumi
Hadaddiyar daular Larababawa UAE ta alanta neman wasu yan Najeriya shida kan laifin ta'addanci.
Yan Najeriyan na ckin jerin mutum 38 da kamfanoni 15 da gwamnatin UAE ta saka cikin jerin sunayen da ke da alaka da ta'addanci, cewar kafar yada labaran Al Arabiya.
A cewar rahoton:
"WAM ta bayyana cewa an yanke wannan shawara ne bisa yunkurin UAE na dakile mutane da kamfanonin dake daukar nauyin ta'addanci da kuma masu alaka da su."
Daga cikin mutane 38 da aka katabta, akwai yan kasar Lebanon 2, yan Yaman 2, yan Syriya biyar, yan Iran 5, yan Iraqi 2, sai kuma yan Indiya, Afghanistan, Britain, Saint Kitts-Navis, Russia, da Jordan .
Ga jerin yan Najeriya shida da ake nema:
Abdurrahaman Ado Musa
Salihu Yusuf Adamu
Bashir Ali Yusuf
Muhammed Ibrahim Isa
Ibrahim Ali Alhassan
Surajo Abubakar Muhammad
Asali: Legit.ng