Tsofaffin tsagerun Neja-Delta sun ba Gwamnatin Buhari wa’adi ta biya su kudinsu ko su dauki mataki

Tsofaffin tsagerun Neja-Delta sun ba Gwamnatin Buhari wa’adi ta biya su kudinsu ko su dauki mataki

  • Tsagerun Neja-Delta da suka ajiye makamai sun ce ba a biya su albashin Agusta ba
  • Tubabban tsagerun sun ce tun da aka nada Kanal Dixion Dikio suke samun matsala
  • ‘Yan kungiyar NDDC za su fara zanga-zanga muddin aka shafe mako ba a biya su ba

Tsofaffin tsagerun Neja-Delta da ke karkashin tsarin lamuni na PAP, sun ba gwamnati wa’adi ta biya su albashinsu na watan Agustan da ya gabata.

Vanguard ta rahoto cewa tubabban tsagerun sun ba gwamnatin tarayya da kuma shugaban PAP, Kanal Dixion Dikio kwanaki bakwai a biya su kudinsu.

Wadannan mutane sun gabatar da kukansu ne ta bakin jagoran kungiyar ‘yan sa-kan Neja-Delta, NDDC, John Egbe a ranar 7 ga watan Satumba, 2021.

Kudin mu sun makale - Egbe

Da yake jawabi a ranar Talata a garin Bomadi, jihar Delta, Janar John Egbe ya zargi Kanal Dixion Dikio da rike albashin tsofaffin tsageru sama da 10, 000.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon sanata

Jaridar ta rahoto John Egbe yana cewa shugaban tsarin lamuni na PAP, Dikio ya hana mutanensa albashi ne ba tare da ya yi bayanin dalilin yin hakan ba.

Tsofaffin tsagerun Neja-Delta
Tsagerun Neja-Delta Hoto: www.newsweek.com
Asali: UGC

“Ofishin bada lamuni ta biya kudinmu na watan Agusta, amma sama da mutane 10, 000 da suke amfana da shirin ba su samu kudinsu ba.”

Dikio ya na neman tada rigima

Kamar yadda jaridar Reuben Abati ta rahoto, Egbe yace Dikio kadai ya san dalilin hana su kudin.

“Tun da Dikio ya shiga ofis muke ganin cin kashi. Wannan karo ba za mu dauki abin da sauki ba, muna so a biya mu kudinmu a mako daya.”
“An samu zaman lafiya a Neja-Delta, amma Dikio da hadiminsa, Alfred Kemepade suna neman tada rigima saboda badakalar da suka shirya”

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa sun fadi ainihin dalilin tsige su Nanono, sun ce ba don Allah aka yi ba

Idan ba a biya masu bukata ba, shugaban kungiyar ta NDDC yace za su fita su yi zanga-zanga. Egbe yayi kira ga shugaban kasa ya yi waje da Mista Kemepade.

Emmanuel Kachikwu ya samu N9.7b?

A yau aka ji Ibe Emmanuel Kachikwu ya roki AGF yayi bincike a kan zargin da ake yi masa na tara Naira biliyan 9.7 a lokacin da yake Ministan man fetur.

Lauyan tsohon Ministan ya rubutowa Ministan shari'a takarda, ya kawo kuka a madadinsa. A cewar lauyan, wasu ne ke neman bata wa Kachikwu suna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel