Mata ta gwangwaje mijinta da dalleliyar mota a ranar cikar aurensu shekaru 7

Mata ta gwangwaje mijinta da dalleliyar mota a ranar cikar aurensu shekaru 7

  • Yayin da maza suke ta gwangwaje matan su da kyautukan ban mamaki, wata mata ta cire tuta
  • Matar ta gwangwaje mijin ta da dalleliyar mota a ranar da auren su ya cika shekaru 7 wanda hakan ya shayar da jama’a mamaki
  • A cewar matar ta ba shi kyautar ne a matsayin sadakin soyayyar su wanda hakan ya burge mutane da dama

Wata mata ‘yar Najeriya ta shayar da mutane mamaki a kafar sada zumunta bayan ta gwangwaje mijin ta da dalleliyar mota a ranar da auren su ya cika shekaru 7.

Matar ta ce sadakin soyayya ne ta bashi wanda hakan ya sa ‘yan Najeriya suka yi ta yaba mata suna cewa gaskiya mace ce ta kwarai.

Mata ta gwangwaje mijinta da dalleliyar mota a ranar cikar aurensu shekaru 7
Matar da ta yi wa mijinta kyautan mota a ranar da suka cika shekaru 7 da aure. Hoto: Adeyemi Holubunmy Crown
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Bayan mako 3 da auren dole, mata mai shekaru 19 ta sheƙe mijin ta a Adamawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk a cikin shagalin zagayowar auren su matar ta nemi faranta wa mijin ta rai kuma ta samu nasarar yin hakan.

Matar mai suna Adeyemi Holubunmy Crown ta ba mijin ta sabuwar mota. Shekaru 7 kenan da auren su kuma sun bayyana farin cikin su ta wannan hanyar.

A wata wallafa ta shafin kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, wata mata ta wallafa wasu kalamai masu taba zuciyar mai karatu yayin da ta hada hakan da hoton wata mota wacce ta ce ta ba mijin ta.

Ta bayyana kyautar ga mijin matsayin sadakin soyayyarta a gare shi

Adeyemi ta ce mijin ta yafi kowa nagarta.

Ta ce sunan mijin na ta Crown Kay Amos kamar yadda ta wallafa:

“Wannan sadakin soyayya ta a gare ka ce. Ina matukar son ka kuma babu abinda zai canja hakan. “Crown Kay Amos ka fi kowa nagarta"

Kara karanta wannan

Malamin addini ya bayyana illar zaɓar miji saboda kyawun sa ba tare da neman zaɓin Ubangiji ba

Mutane sun yi tururuwar yin tsokaci inda suka yita yabon matar.

Ella Firstlasy tayi tsokaci ta ce:

“Barka Mama... Muna fatan ci gaba da ganin irin hakan albarkacin Jesus, amen. Daddy za ka ci gaba da zama shugaba ba mabiyi ba.”

Kemmy Kayode ya ce:

“Barkan ku da zagayowar shekarun auren ku, ina fatan soyayyar ku ta kasance har abada. Madam, kinyi kokari. Kuma kin nuna wa jinsin mu cewa ke matar da ya dace a aura ce.”

Olagbemiro Akinmerese Funmilayo ya ce:

“Barka da zagayowar shekarun auren ku... Ubangiji ya ci gaba da albarkatar gidan ku. Ku samu zuri’a mai nagarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164