Yanzu-yanzu: DPO na 'yan sanda a Katsina ya gwabza hatsari, ya ce ga garin ku

Yanzu-yanzu: DPO na 'yan sanda a Katsina ya gwabza hatsari, ya ce ga garin ku

  • DPO na ofishin 'yan sandan karamar hukumar Musawa a jihar Katsina ya rasa ran sa sakamakon hatsarin mota
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce marigayin ya rasu ne yayin da ya ke hanyar komawa Musawa daga Katsina
  • Bai wuce sauran kilomita goma tsakaninsa da garin ba ya gwabza hatsari inda ya ci karo da babbar mota wanda a take ya rasu

Musawa, Katsina - DSP Sabo Umar, DPO na ofishin 'yan sandan karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina ya rasu sakamakon mummunan hatsarin motan da ya gwabza. Mummunan lamarin ya auku a ranar Laraba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce marigayin dan sandan ya na dawowa zuwa Musawa daga Katsina bayan halartar taro da kwamishinan 'yan sandan jiha tare da sauran cibiyoyin tsaro yayin da hatsarin ya auku.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Yanzu-yanzu: DPO na 'yan sanda a Katsina ya gwabza hatsari, ya ce ga garin ku
Yanzu-yanzu: DPO na 'yan sanda a Katsina ya gwabza hatsari, ya ce ga garin ku
Asali: Original
"Marigayin DPO ya zo nan tare da sauran jami'ai, DSS da wasu jami'an cibiyoyin tsaro domin tabbatar da sabbin tsarin ayyuka wadanda gwamnatin jihar Katsina, kwamishinan 'yan sanda, CP Sanusi Buba, a matsayin shugaban kwamitin ayyukan.
"Bayan taron, yayin da ya ke hanyarsa ta zuwa Musawa, kilomita 10 ta rage, ya na karamar hukumar Matazu, ya ci karo da babbar mota wanda a take ya rasa rayuwarsa," Isah ya ce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa, gawar marigayin dan sandan an fara adana ta a babban asibitin Katsina kafin a kai ta karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto domin birne shi.

Isah ya mika godiyar rundunar ga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, kan taimakon iyalan mamacin da yayi, Daily Trust ta ruwaito.

Wadanda ake zargi sun sanar da dalilinsu na sacewa da sheke mahaifin tsohon gwamna

Kara karanta wannan

Cikin Sauki Sojoji Ke Maganin Yan Bindiga Tun Bayan Datse Sabis a Zamfara, Kwamishina

A wani labari na daban, makasan Pa Defwan Dariye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye sun bayyana cewa sun yi garkuwa da shi ne don su samu kudade daga hannun dan sa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce Jethro Nguyen mai shekaru 53 dan asalin Bakos da ke jihar Filato ne ya hallaka Dariye.

Daya daga cikin su mai suna Sunday Ibrahim, ya kara tabbatar da cewa Nguyen ne wanda ya shirya komai don shi yayi hayar mutane 10 don su yi garkuwa da tsohon har fadar sa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel