Fadar Shugaban kasa ta saki hotunan ziyarar da Buhari ya kai Owerri, jihar Imo
Imo - A ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar ta musamman babbar birnin jihar Imo, Owerri.
Buhari ya amsa gayyatar da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, yayi masa domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta kammala.
Buhari ya samu kyakkyawan tarba daga wajen gwamnan jihar, Hope Uzodinma, wanda ya gayyacesa da kuma al'ummar jihar Imo duk da cewa kungiyar IPOB ta umurci jama'a kada su sake su fito.
Shugaban kasan ya ce ya ga abin da ya isa a jinjina wa namijin kokarin Gwamna Hope Uzodinma.
Shugaban kasar ya ce manyan ayyukan shugaban na jihar Imo ya birge shi duk da yanayin da ake ciki.
Na ga abubuwan da suka tabbatar da mutuncin Uzodinma, cewar Buhari yayin da ya kaddamar da ayyuka a Imo
A Imo, Buhari ya kaddamar da titin kasa mai kwalbeti na zamani, (Chukwuka Nwoha), Titin Naze, da titin Nekede/Ihiagwa.
Hakazalika ya kaddamar da sabon farfajiyar taron majalisar zartaswar jihar da kuma Egbeada Bypass (Amakohia).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli hotunan ziyarar:
Asali: Legit.ng