Gwamnan Katsina ya haramta sana'ar cajin waya a jiharsa
- Gwamnan Kastina ya bada umurnin kulle shagunan cajin waya a wasu kananan hukumomin jihar
- Masari ya ce wannan zai taimaka wajen rage matsalar tsaro a jihar
- Gwamnan ya kafa kwamiti na musamman don tabbatar da bin wannan dokan
Cikin yunkurin kawo karshen matsalar tsaro, Gwamnan jihar Katsina, Malam Aminu Bello Masari, ya haramta sana'ar cajin waya a kananan hukumomi 18 cikin 34 na jihar.
Masari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin rantsar da kwamitin da aka kafa don tabbatar da ana biyayya ga sabbin dokoki 10 da gwamnatin jihar tayi.
An rantsar da kwamitin ne a gidan gwamnatin jihar dake birnin Katsina, rahoton ChannelsTV.
Masari na ganin cewa wannan sabon doka na hana sana'ar cajin waya a wadannan kananan hukumomi zai taimaka wajen rage matsalar tsaro.
A cewarsa:
"Umurnin karshe da muka bada shine kulle dukkan shagunan cajin wayoyi a kananan hukumomin da matsalar tsaro tafi shafa. Muna da fahimtar cewa sana'ar cajin waya na taimakawa yan bindiga wajen sadarwa."
"Mun yi imanin cewa wannan mataki da kuma wasu matakai da muka dauka tare da ma'aikatar sadarwa zasu taimaka wajen kawo sauyin lamari a garuruwan."
Kananan hukumomin da wannan dokar zata shafa sune Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Paskari, Sabuwa, Kurfi, Danja, Kaita, Bakori, Funtua, Kankara, Musawa, Matazu, Dutsima, Mai’adua, Malumfashi da Funtua.
Asali: Legit.ng