Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 6 hannunsu, yan bindiga sun saki yayan sakataren jihar Katsina
- Gwamnatin Katsina ta saki mahaifin shugaban yan bindiga don su saki yayan sakataren jihar
- Yan bindigan sun sace yayan sakataren ne kimanin mako daya da ya gabata
- Gwamnatin jihar ta kafa sabbin dokokin kawo karshen matsalar tsaro
Katsina - Kabir Muhammad, Yayan sakataren gwamnatin jihar Katsina, Muhammad Inuwa, da aka sace ranar Larabar da ta gabata, ya samu yanci bayan kwanaki shida.
Mai magana da yawun Inuwa, Kabir Yar'adua, ya tabbatar da hakan ranar Talata, rahoton Punch.
Yace:
"Lallai an saki dattijon amma babu kudin da aka biya na fansa."
An samu labarin cewa an saki dattijon ne bayan damke wasu masu kaiwa yan bindiga bayanai a jihar, cikinsu har da mahaifin shugaban yan bindigan.
Majiyoyi sun bayyana cewa an tuntubi yan bindigan cewa an damke mahaifin shugabansu, sai yan bindigan suka yarda a sake yayan SSG Inuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya ta bayyana cewa,
"Yan bindigan sun saki Yaya Muhammad da daren Litinin kuma ya koma wajen iyalansa."
"Ba'a biya kudin fansa ba, saboda mun saki mahaifin shugaban yan bindigan a maimako bayan sun saki namu."
Kakakin hukumar yan sandan jihar dai, SP Gambo Isah, bai tabbatar da labarin ba tukun.
Asali: Legit.ng