Katsina: 'Yan bindiga sun tafi har gida sun sace 'ya'yan mataimakin shugaban Kwallejin Ilimi

Katsina: 'Yan bindiga sun tafi har gida sun sace 'ya'yan mataimakin shugaban Kwallejin Ilimi

  • 'Yan bindiga sun sace 'ya'yan shugaban kwallejin Ilimi ta Isa Kaita da ke Dutsinma Jihar Katsina
  • 'Yan bindigan sun afka makarantar ne cikin dare suka nufi gidan Dr Ismaila Ado Funtua amma suka tarar baya gida
  • Bayan ganin baya gida sai suka sace yaransa uku da kuma mai gadin makarantar amma daga bisani suka saki mai gadin

Jihar Katsina - Yan bindiga sun kutsa cikin Kwallejin Ilimi na Isa Kaita da ke Dutsinma, Jihar Katsina sun sace 'ya'yan Dr Ismaila Ado Funtua, mataimakin shugaban makarantar, Daily Trust ta ruwaito.

Wani majiya na kusa da Ado Funtua ya tabbatarwa Daily Trust afkuwar lamarin.

Katsina: 'Yan bindiga sun tafi har gida sun sace 'ya'yan mataimakin shugaban Kwallejin Ilimi
Yan bindiga: Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Shekara daya bayan sace shi, 'yan bindiga sun sace iyalan dan majalisa a Katsina

Majiyar ya ce 'yan bindiga dauke da muggan makamai ne suka kutsa makarantar a daren ranar Litinin.

Majiyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"A lokacin da suka iso, mai tsare kofar makarantar baya nan. Sun cire kwadon da ke jikin kofar suka shiga gidan.
"A yayin da suke gidan, mai tsaron kofar ya dawo suka tambaye shi ina mai gidansa kuma ya ce baya nan.
"Sun shiga cikin gidan suka tarar da yara suna karatu. Sun sace mai gadin tare da yara guda uku, Usman, Aminu da Abdullahi, yayin da yaron na hudu ya sulale ya tsere."

Majiyar ta kara da cewa, a hanyarsu na fita, masu garkuwar sun sako mai gadin suka tafi da 'ya'yan mutumin.

Yan bindiga sun sace 'ya'yan dagaji a Katsina

Hakan ya faru ne bayan yan bindiga sun kai hari wani unguwa a Katsina sun sace yaran dagajin kauyen su hudu.

Yan bindigan sun kutsa kauyen Sabuwar Kasa a karamar hukumar Kafur na Jihar Katsina a safyar Litinin sun sace yaran Alhaji Hamza Umar.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Gida Sun Sace Mahaifi Da Ɗansa a Abuja

Umar, dagajin sabuwar Kasa kuma shine shugaban karamar hukumar Funtua a jihar.

Ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo ba a lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel