Jigo a ƙungiyar Arewa ta ACF ya yanke jiki ya faɗi matacce a ofis

Jigo a ƙungiyar Arewa ta ACF ya yanke jiki ya faɗi matacce a ofis

  • Allah ya yi wa Sakataren Gudanarwar Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), Alhaji Mohammed Sani Soba, rasuwa
  • Alhaji Mohammed Sani Soba ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi a ranar Asabar, 4 ga Satumban 2021
  • Sakataren Yada Labaran ACF na kasa, Emmanuel Yawe, ya tababtar da rasuwar a ranar Talata yana mai cewa kowa a ACF ya yi alhinin rashin Soba

Jihar Kaduna - Sakataren Gudanarwa na ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa wato Arewa Consultative Forum, Alhaji Mohammed Sani Soba, ya riga mu gidan gaskiya.

SaharaReporters ta ruwaito cewa Sani Soba ya yanke jiki ya faɗi ne a hedkwatar kungiyar da ke Kaduna.

Jigo a ƙungiyar Arewa ta ACF ya yanke jiki ya faɗi matacce a ofis
Tambarin Kungiyar Tuntuba ta Arewa, ACF. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Sakataren ACF, Emmanuel Yawe ya tabbatar da rasuwar Alhaji Sani Soba

Sakataren watsa labarai na ƙasa na kungiyar ACF, Emmanuel Yawe, ne ya sanar da rasuwarsa a ranar Litinin kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan yada labarai a lokacin mulkin Janar Babangida ya rasu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce Sabo wanda ya riga mu gidan gaskiya tsohon sakataren dindindin ne a gwamnatin jihar Kaduna kafin ya yi ritaya.

A cewarsa;

"Alhaji Soba yana aiki da ACF ne a kan kwantiragi. An haifi marigayin ne a 1949 kuma ya samu satifiket ɗin kammala frimari a 1964."
"Ya cigaba da karatu a gida da kasashen waje a ɓangarori daban-daban musamman harkar mulki da yin dokoki."

Yawe ya cigaba da cewa:

"Daga bisani ya zama Akawu na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna. An yi alhinin mutuwarsa a sakatariyar ACF inda ya ke rike da mukamin shugaban gudanar da mulki kafin rasuwarsa."

'Dan Nigeria Mai Tallan Mangwaro Ya Samu Gurabe 6 Don Zuwa Ƙasar Waje Yin Digirin Digirgir Kyauta

A wani labarin daban, wani dan Najeriya, Onyeka Chukwudozie ya samu tayin karatun digirin-digirgir daga jami’o’i 6 daban-daban dake Australia da California, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya cilla kasar waje ziyarar aiki

Matashin ya bayyana wannan nasarar ne ta shafin sa ba Linkedln inda ya ce har tallar magwaro da lemu ya yi a kasuwanni a baya.

A cewar sa, ya samu wannan damar cigaba da karatun ne bayan jami’o’i da dama sun hana shi cigaba da karatu a shekarun baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel