Da Ɗuminsa: 'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban NBC da 'yarsa a Katsina

Da Ɗuminsa: 'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban NBC da 'yarsa a Katsina

  • Masu garkuwa da mutane sun sace tsohon direktan NBC, Ahmed Abdulkadir da yarsa a Katsina
  • Hakan na zuwa ne kasa da awa 24 bayan wasu yan bindigan sun sace iyalan dan majalisar dokokin jihar Katsina
  • Baya ga tsohon direktan, yan bindigan sun sace wasu mutane uku amma sun sako su bayan yan banga sun yi musayar wuta da su

Katsina - Kimanin kwana guda bayan sace iyalan dan majalisar dokokin jihar Katsina, 'yan bindiga sun sake sace wasu mutanen a jihar.

A cewar rahoton Daily Trust, a daren jiya, yan bindigan sun kai hari rukunin gidaje na Bakori sun sace wani Alhaji Ahmed Abdulkadir, tsohon direktan NGC da yarsa mai shekaru 15 mai suna Laila.

Da Ɗuminsa: 'Yan bindiga sun sace tsohon shugaban NBC da 'yarsa a Katsina
Taswirar Jihar Katsina. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wani sarkin gargajiya a jihar Neja

Yan bindigan da suka taho da AK-47 sun kuma sace wasu mutane guda uku.

Sun kai hari gidajen wadanda abin ya faru da su ne misalin karfe 9 na dare a cewar majiyoyi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sauran da aka sace sun hada da Alhaji Bello Aminu Bakori, Shamsuddeen Aminu da wani Habibu Rabe ma'aikacin hukumar Ilimi, Bakori.

'Yan banga sun sun ceto mutane uku daga hannun 'yan bindigan

Jim kadan bayan sace su, 'yan banga da ke unguwar sun taru sun bi sahun bata garin da nufin ceto wadanda aka sace.

Yan bangan sun cimma yan bindigan a karamar hukumar Danja kuma bayan musayar wuta sun sako uku cikin wadanda suka sace.

Amma Abdulkadir da yarsa har yanzu suna nan hannun masu garkuwar.

Yan bindigan sun saka mutane cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren da suke kai wa a yankunan kasar.

Daga Abuja, zuwa Zamfara, Niger, Kaduna da wasu wuraren da dama, yan bindigan su kan kutsa gidajen mutane su sace su domin karbar makuden miliyoyi na fansa.

Kara karanta wannan

Shekara daya bayan sace shi, 'yan bindiga sun sace iyalan dan majalisa a Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel