Zaben APC: 'Yan taware da ke tare da Buhari, sun bijirewa APC, Ganduje a Kano

Zaben APC: 'Yan taware da ke tare da Buhari, sun bijirewa APC, Ganduje a Kano

  • Wani bangare na jam'iyyar APC masu biyayya ga Buhari sun aiwatar da zaben shugabannin jam'iyyar a matakin kananan hukumomi a jihar Kano
  • Bangaren ya samu shugabancin Shehu Dalhatu, shugaban kungiyar goyon bayan Buhari inda ya samu goyon bayan wadanda ba su ga-maciji da Ganduje
  • Kamar yadda 'yan tawaren suka bayyana, sun yi zabe ne irin na damokaradiyya ba wai na son zuciya ba da son rai kamar yadda wasu ke yi

Kano - Rikici ya mamaye tarukan jam'iyyar APC na kananan hukumomi a jihar Kano yayin da mambobin kungiyar goyon bayan Buhari, wani bangare na jam'iyyar suka yi tarukan majalisa a kananan hukumomi 44 a ranar Asabar da ta gabata a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda kwamitin rikon kwarya mai samun jagorancin Abdullahi Abbas na jam'iyyar ya yi taron masu ruwa da tsaki tare da Gwamna Abdullahi Ganudje, inda suka yanke hukuncin tsayar da cancantattun 'yan takara domin shugabancin jam'iyyar a matakin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Zaben APC: 'Yan taware da ke tare da Buhari, sun bijirewa APC, Ganduje a Kano
Zaben APC: 'Yan taware da ke tare da Buhari, sun bijirewa APC, Ganduje a Kano. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Amma kuma wasu mambobin kungiyar goyon bayan Buhari, BSO, wacce ta samu shugabancin Shehu Dalhatu, ta yi watsi da wannan shirin inda ta yi taron majalisa har ta samu zababbu 27 a kowacce karamar hukuma ta jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

A yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron a karamar hukumar Tofa ta jihar, dan majalisa mai wakiltar mazabar Tofa, Rimin-Gado/Dawakin Tofa a tarayya, Tijjani Jobe ya ce jam'iyyar ta yi zaben ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jobe, wanda ba su ga-maciji da Ganduje, ya kushe abinda ya kwatanta da "yarjejeniyar son kai wacce wasu tsirarun mambobi suka yi da sunan damokaradiyya."

"Ba a yin zaben jam'iyya a dakin ka ko a gidan gwamnati. Ya dace ku koma ga jama'a su yanke hukuncin abinda su ke so. Dole ne kowanne dan jam'iyya ya zamo a ciki.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023

"Idan ka hana jama'a shiga, hakan ya na nufin ba damokaradiyya ba ce. Amma kuma abinda muke ta ikirari shi ne damokaradiyya.
"Toh abinda mu ke yi yanzu shi ne barin jama'a su zaba da kansu ba wai abinda mu ke so ba," Joobe ya ce.

Kano: Dan kwangila ya kai shugaban karamar hukuma kara wurin EFCC kan rike mishi N14.9m

A wani labari na daban, wani dan kwangila, Mustapha Umar-Tallo ya mika takardu 2 zuwa ofishin hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ya na zargin shugaban karamar hukumar Gwarzo, Bashir Abdullahi da kin biyan shi kudaden kwangilar da yayi na karamar hukumar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Umar-Tallo, ya rubuta takardar ta lauyan sa, Abubakar Lagazab, inda ya ke zargin shugaban karamar hukumar da kin biyan su kudaden duk da gwamnatin jihar ta riga ta biya kudaden.

A takardar ta ranar 17 ga watan Nuwamba 2020 wacce ya bayyana ta ga manema labaran jihar Kano a ranar Alhamis, Umar-Tallo ya zargi shugaban karamar hukumar da lamushe kudaden ayyuka 20 na kwadago da ayyuka 14 na karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

Asali: Legit.ng

Online view pixel