Dattawan arewa: Garkame wasu yankunan arewa zai sake tsananta matsaloli

Dattawan arewa: Garkame wasu yankunan arewa zai sake tsananta matsaloli

  • Kungiyar dattawan arewa ta NEF ta ce sanya kulle da kuma katse sadarwa za su kara tsananta rayuwa ne a arewacin Najeriya
  • A matsayin hanyar gyara tsaro, wasu gwamnonin jihohin sun rufe kasuwanni da makarantu a arewa
  • A ranar Asabar, ma’aikatar sadarwa ta umarci duk kamfanonin sadarwa su dakatar da hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara

Kungiyar dattawan arewa ta NEF ta ce dakatar da sadarwa a arewacin Najeriya da kuma sanya kulle za su kara tabarbara harkokin tsaro.

TheCable ta ruwaito cewa, a matsayin hanyar gyara tsaro, wasu gwamnonin jihohi sun rufe makarantu da kasuwanni a jihohi.

Dattawan arewa: Garkame wasu yankunan arewa zai sake tsananta matsaloli
Dattawan arewa sun kushe garkame jihar Zamfara da kuma katse hanyoyin sadarwa da aka yi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A ranar Asabar, ma’aikatar sadarwa ta NCC ta umarci duk kamfanonin sadarwa su dakatar da sadarwa a jihar Zamfara sakamakon hauhawar rashin tsaro a jihar.

A ranar Lahadi, kakakin NEF, Hakeem Baba-Ahmed ya ce wannan matakin zai iya tsananta rashin tsaron, TheCable ta wallafa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Najeriya ya ba ma’aikata wa’adin kwanaki 14 don yin allurar korona

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kungiyar dattawan arewa, bayan ganin farmaki da dama da ta ke ganin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane suke kai wa arewacin Najeriya ta yi wani nazari,” kamar yadda takardar ta zo.
“Wasu gwamnatin jihohi sun dauki wasu matakai kamar dakatar da kasuwannin makonni, rage yawan fetur din siyarwa, rufe makarantu da wasu titina, sanya kulle, dakatar da yawon shanu da kuma dakatar da sadarwa a bangarorin da rashin tsaro ya fi tsananta duk da halin da suke ciki.
“Sam wannan ba zai taimaka ba wurin kawo dauki ga mutanen da suke cikin tashin hankali irin wannan.Ya kamata gwamnati ta kawo wasu hanyoyin da za su taimaka musu ne ba su cutar da su ba.
“Wadannan hanyoyin za su rushe tattalin arzikin mutanen da ‘yan ta’adda suka tasa gaba kuma su dakatar da su daga sanar da matsalolin su.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara

“Sai an dauki tsauraran matakai a kan ta’addanci da gafarta wa mutane sannan jama’a za su kubuta.
“Babban abinda za su yi shi ne su cigaba da ta’addanci sannan gwamnati da jami’an tsaro ba za su iya yin komai ba a wuraren da aka sa kulle. Wuraren da suke fama da rashin tsaron za su cire rai daga gwamnatin jiharsu da jami’an tsaro.”

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo sassauci ga jihohin da aka tsananta wa rayuwa.

ISWAP ta yi ikirarin harba rokar Katyusha a Mallam Fatori sau 4 a mako 1

A wani labari na daban, mayakan ISWAP wadanda aka fi sani da Boko Haram sun harba roko zuwa Mallam Fatori da ke jihar Borno har sau hudu a cikin mako daya tak.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan sun kai wa sansanonin farmaki a harin wanda ya yi sanadiyyar salwantar sojoji 5.

Kara karanta wannan

NCC: Babu maganar dawo da Twitter yanzu duk Najeriya tayi asarar Naira Biliyan 200

A wata takarda wacce IS ta saki a ranar 1 ga watan Satumba, ‘yan ta’addan ISWAP sun ce sun dade suna harba roka sansanin soji da ke Mallam Fatori kuma sun hallaka sojoji 4 kenan tun ranar 25 daga watan Augusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel