Gwamnan Najeriya ya ba ma’aikata wa’adin kwanaki 14 don yin allurar korona
- Gwamnatin jihar Ondo ta ba da sanarwar cewa za ta aiwatar da sabbin matakai don hana yaduwar cutar ta COVID-19
- An shawarci ma’aikatan gwamnati a jihar da su kasance masu bin ƙa’idar COVID-19
- Cutar korona ta sake bulla a wasu jahohi a fadin kasar nan
Gwamna Rotimi Akeredolu ya umarci ma’aikatan gwamnati a jihar Ondo da su yi rigakafin COVID-19 a cikin makonni biyu.
An bayar da wannan umarnin ne a ranar Juma’a, 3 ga watan Satumba, a cikin wata takardar da OJ Afolabi, babban sakatare, mai kula da harkokin hidima ya sanya wa hannu, a madadin shugaban ma’aikatan gwamnati na Ondo, jaridar ThisDay ta ruwaito.
Gwamnatin ta bayyana cewa daga yanzu ma’aikatan gwamnati za su bayar da katunan shaidar rigakafi kafin a ba su damar shiga wasu wuraren.
Sanarwar tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
''Gwamnatin jihar Ondo ta sanya allurar rigakafin COVID-19 ya zama tilas ga dukkan ma'aikatan jihar.
“A cikin daftarin gwamnati wanda Sakataren dindindin na harkokin ma’aikaya, Mista O.J. Afolabi, a madadin shugaban ma’aikata, gwamnatin jihar ta ba ma’aikatan gwamnati a jihar makonni biyu su dauki allurar rigakafin.”
A wani labari na daban, hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su katse hanyoyin sadarwarsu a jihar Zamfara, Daily Nigerian ta ruwaito.
A daya daga cikin wasikun da aka aike wa kamfanonin, mataimakin shugaban hukumar Umar Danbatta a ranar Juma'a 3 ga watan Satumba ya ce matakin na daya daga cikin dabarun da jami'an tsaro ke bi na dakile 'yan bindiga da ke addabar jihar.
Asali: Legit.ng