Tsohon ‘Dan wasan Real Madrid ya bada labarin wani fadan Ronaldo da Jose Mourinho

Tsohon ‘Dan wasan Real Madrid ya bada labarin wani fadan Ronaldo da Jose Mourinho

  • Angel Di Maria yace an taba rigima tsakanin Jose Mourinho da Cristiano Ronaldo
  • Mourinho ya horas da Cristiano Ronaldo da Angel Di Maria a lokacin suna Madrid
  • Di Maria yace an yi ranar da rashin jituwa ya shiga tsakanin Tauraron da Kocinsa

Paris - Tauraron Paris Saint-Germain, Angel Di Maria ya bada labarin wata rigima da ta taba kaure a tsakanin Jose Mourinho da Cristiano Ronaldo.

Angel Di Maria yace Kocin ya taba samun sabani da babban ‘dan wasan Duniya, Cristiano Ronaldo.

Metro ta rahoto Di Maria yana bada labarin abin da ya wakana tsakanin 2010 da 2012 a lokacin da Mourinho ya horas da ‘yan wasan Real Madrid.

Mourinho ya horas da Real Madrid

Kara karanta wannan

Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi da kasar Portugal a Duniyar wasan kwallon kafa

Mourinho ya yi aiki na shekaru uku a Madrid, a lokacin ‘dan wasa Ronaldo yana ganiyarsa bayan an dauko shi daga kungiyar Manchester United.

Duk da cewa dukkaninsu ‘yan kasar Portugal ne, Ronaldo ya yi rigima da kocin a dalilin sukarsa da ya yi, kuma ya yi masa gori a kan ilmin bokonsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda jaridar ta rahoto, Di Maria wanda yanzu yake buga wa PSG tare da Lionel Messi, yace Jose Mourinho zai iya yin fada da ko wanene.

Ronaldo da Jose Mourinho
Ronaldo da Mourinho a Real Madrid Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

“Mourinho bai da hankali.”

“Mourinho bai da hankali. Idan yana hulda da ni, kullum a mutum kirki yake. Yan a fada da kowa, babu ruwansa da ko wanene.”
“Wata rana ya yi rigima da Ronaldo, yake fada masa ba ya gudu, a lokacin da kowane ‘dan wasa yake zura guda saboda shi.”

Kara karanta wannan

NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe

A Real Madrid, akwai lokacin da aka ga Ronaldo ya samu sabani da kocin na sa bayan kungiyarsa ta samu jan kati yayin da take buga wasa da Barcelona.

Ronaldo ya fi kowa kwallaye a gida

A daren Alhamis ne Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi da kasar Portugal a Duniyar wasan kwallon kafa, tauraron ya ci kwallayensa na 110 da 111.

Tsohon ‘dan wasan na Juvenuts shi ne ‘dan wasan da ya fi kwallaye a kasarsa, ya doke Ali Daei.

Asali: Legit.ng

Online view pixel