NLC: ‘Yan kwadago suna barazanar tafiya yajin-aiki a kan yunkurin kara kudin lantarki
- Kungiyar NLC ta nuna ba ta goyon bayan ayi karin kudin wutar lantarki
- Shugaban NLC, Ayuba Wabba ya nuna za su iya tafiya yajin-aiki a kasar
- Wabba yace an yi alkawari gwamnati ba za ta kara kudin wuta yanzu ba
Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa, NLC tace za ta kira yajin-aiki idan har gwamnatin tarayya ta dabbaka sabon tsarin biyan kudin shan wutar lantarki.
Jaridar Punch ta rahoto cewa NLC ta tuna wa gwamnatin tarayya alkawarin da suka yi a Satumban 2020.
Kungiyar ‘yan kwadagon ta fadakar da Ministan kwadago, Chris Ngige cewa an yi yarjejeniya ba za a kara kudin lantarki ba sai an gama zaman da ake yi.
Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago sun kafa kwamiti da ke zama kan batun farashin wutar lantarki tun 2020, har yau kwamitin bai gama aiki ba.
Ayuba Wabba ya yi magana
Shugaban NLC na kasa, Kwamred Ayuba Wabba ya ja-kunnen gwamnatin tarayya bayan samun labari cewa an ba kamfanoni wuta dama su kara farashi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Muna bukatar mu jawo hankalinku ga rade-radin da ke bin gari, musamman game da rahoton sabon karin farashin da aka ba kamfanoni dama su yi.”
“Mun rubuta takarda domin mu tuna wa Mai girma Minista cewa a ranar 28 ga watan Satumba, 2020, kwamitin kwadago ya yarda a janye batun karin kudin shan wuta har sai kwamiti ya kammala aikinsa, shugabannin kwamiti sun karbi aikin.”
Matakin da NLC za ta dauka
“A dalilin wannan, muka yi watsi da rahoton karin kudin wutan a matsayin jita-jita kurum.”
“Sai dai mun ga bukatar mu sanar da kai muddin gwamnati ta amince da sabon farashi, babu abin da zai rage mana sai mu yi yaji, mu kare hakkinmu.”
Kamar yadda Premium Times a fitar da rahoto a ranar Laraba, shugaban NLC yace doka ta ba su hurumin da za su shiga yajin-aiki domin kare hakkin ma’aikata.
Rade-radin kudin shan wuta zai tashi
A farkon shekarar nan Festus Keyamo ya yi magana game da rade-radin karin kudin wuta. Karamin Ministan yace abin da aka yi ba karin farashi bane.
Da yake bayani, Festus Keyamo ya bayyana cewa an yi wasu ‘yan kwaskwarima ne kurum a kan kudin shan wutan, amma lamarin bai kai ga karin farashi ba.
Asali: Legit.ng