Dalla-dalla: Yadda Adam Zango ya so auren Ummi Rahab, Yasir M Ahmed yayi bayani

Dalla-dalla: Yadda Adam Zango ya so auren Ummi Rahab, Yasir M Ahmed yayi bayani

  • Matashin nan, Yasir, marikin Ummi Rahab ya yi karin haske game da ikirarin da ta yi na tona wa Adam Zango asiri
  • Kamar yadda yace tabbas Zango ya bayyana soyayyarsa ga Ummi kuma har wurin mahaifiyarta a Saudiyya ya je domin aurensu
  • A cewarsa, ya sanar da duk wasu manyansu amma suka nemi Zango suka rasa kuma bai sake tayar da maganar aurensu ba har yau

Kano - A wani bidiyo da Yasir, marikin Ummi Rahab ya musanta maganar Adam Zango inda yace bai taba yin soyayya da matashiyar jarumar ba, kuma ya rabu da ita ne saboda ba ta yi masa biyayya.

Matashin mai suna Yasir M. Ahmad, wanda yace shi dan uwan jarumar ne, ya bayyana a wani bidiyo mai tsawon minti 20 yana kora jawabin.

Da farko Adam Zango ya so auren Ummi Rahab, Yasir M Ahmed ya yi bayani
Da farko Adam Zango ya so auren Ummi Rahab, Yasir M Ahmed ya yi bayani. Hoto daga @official_adam_zango da @official_ummi_rahab
Asali: Instagram

Ya fara da cewa sam Adamu ba shi ne ya kai Ummi Rahab industiri ba, sun hadu ne a shirin fim din ‘Ummi’.

Ya kara da bayyana yadda sam Zango ba ya da wata alaka da yarinyar ta jini, nesa ko kusa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yace:

Na farko dai, Adamu ba shi ya kawo Ummi industiri ba, kuma ba ya da alaka ta family ko wani dangi na nesa ko na kusa. Hasalima sun hadu a shirin fim din Ummi ne, ta zo ya zo.

Yasir ya kara da cewa:

Bayan an gama aikin ne mu ka yi musayar lambobin waya. To wannan shi ne haduwar su na farko da Zango.

A cewarsa:

Bayan sati biyu Adamu ya kira shi. Yana ce min sun saba da dan sa Haidar kuma yana neman alfarma idan ta yi hutu yana so ta zo gidansa ta yi hutu. Bayan nan ne naje har Kaduna na kai masa yarinyar na bar ta kuma bayan sati biyu ya dawo da ita gida.

A cewarsa lokacin da Adamu zai je saudiyya shi da Afakallahu da Rarara, sun amshi lambar wayar mahaifiyarta kuma sun je sun gaisa da ita domin batun aurensu.

Sai dai har a halin yanzu, Adam Zango bai sake tada maganar auren ba kuma yana hana ta yin samari balle ta samu wani mijin da zai aure ta.

Zamfara: Ƴan bindiga sun sheƙe rai 1, sun tasa keyar 7 kan ƙin biyan haraji

A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga sun sheke mutum 1 kuma sun tasa keyar mutum bakwai a kauyukan Dadah, Tukurawa da Gandamasu a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Premium Times ta ruwaito cewa, miyagun 'yan bindigan sun kai farmaki kauyukan a daren Alhamis sakamakon kin biyan haraji da mazauna kauyen suka yi wanda 'yan bindigan suka kallafa musu.

Zurmi tana daya daga cikin kananan hukumomi a jihar Zamfara da 'yan bindiga suka gallaba. Suna da iyakoki da karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel