Bidiyon wani mutum da Zakuna suka rungume bayan shekaru 7 da ya ceci rayuwarsu
- Wani mutum mai suna Kevin Richardson, ya daukar wa kan shi alkawarin zuwa ganin Zakunan da ya ceta shekaru 7 da suka gabata
- Kamar yadda Kevin wanda ke da wurin kiwon Zakuna ya sanar, ya saba rainon kananan zakuna a lokutan da iyayensu suka ki su
- A wani bidiyo da aka dauka yayin haduwar Kevin da Zakunan, sun hadu ne a cikin ruwa kuma sun rungume juna har da sumbatar juna
South Africa - Wani mutum ya ci karo da Zakunan da ya ceci rayuwarsu a shekaru 7 da suka gabata, haduwar ta baiwa jama'a da yawa mamaki.
Kevin Richardson mamallakin wurin kiwon Zakuna a kasar Afrika ta kudu wanda ya dauka hatsarin haduwa gaba da gaba da Zakunan domin ya tabbatar da cewa ko sun gane shi.

Asali: UGC
OMG Newss ta ruwaito cewa Kevin ya taimaka Zakunan yayin da mahaifiyarsu Zakanya ta ki karbarsu a matsayin 'ya'yanta.
An gano cewa ya kusanci Zakunan har zuwa inda suke zama kuma ake kula da su.
Haduwa mai tarin hatsari
A wani bidiyon YouTube da Go Pro VR BTS suka nada tare da wallafa shi, Kevin ya ci karo da zakunan masu suna Meg da Ammy a wani rafi kuma gadan-gadan ya nufe su.
Ya kira sunan daya da ciki yayin da yake matsawa kusa dasu da sauri. A take zakin ya gane wanda ya raine shi kuma ya fada kan shi. Tuni Zakin ya rungume mutumin tare da sumbatarsa.
Budurwa ta sanar da yadda saurayi ya fara surkullen tsafi yayin da ya ke kokarin cewa ya na son ta
A wani labari na daban, wata budurwa ‘yar Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook kan yadda wani mutum ya fara surkullen tsafi bayan ya ganta a titi yana kuma son ya bayyana mata soyayyarsa.
Morenikeji Adekunle Praiseberry, ta bayyana yadda ta bar diyar ta da kakar ta a gida lokacin da ta fita ciro kudi a banki, tace kawai ta ji wani yana bin ta kamar yana so yayi mata magana yana ta kusantar ta, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Ta ce ta ji lokacin da yake ta surkullen tsafi sannan ya umarce ta da ta bishi, tana jin tana son bin shi amma sai ta tuna ba ta san shi ba, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Asali: Legit.ng