Sojan da yan bindiga suka sace a NDA na nan da ransa, bai mutu ba: FIJ

Sojan da yan bindiga suka sace a NDA na nan da ransa, bai mutu ba: FIJ

  • Sabanin rahotannin mutuwarsa, ana kyautata zaton Manjo Dantong na raye
  • Wadanda sukayi magana da yan bindigan sun ce sun yi magana da shi
  • Hukumar Soji ba tayi magana kan lamarin har yanzu ba

Kaduna - Duk da rahotannin cewa ya mutu, rahotanni daga iyalan Manjo Dantong da aka sce sun bayyanawa FIJ cewa har yanzu yana nan da ransa bai mutu ba.

Yan bindiga sun yi awon gaba da Mano Dantong ne cikin daren Talata lokacin da suka kai hari makarantar Soji ta NDA dake Afaka, jihar Kaduna.

Bayan shi da aka dauke, yan bindigan sun kashe Sojoji biyu.

Kafafen yada labarai da dama sun ruwaito cewa sun kashe Manjo dantong amma iyalan Sojan sun ce yan bindigan sun basu hujjar dake nuna yana raye.

A cewar rahoton FIJ, yan bindigan sun bukaci Sojan ya fada musu sunan mutum daya da zasu rika kira kuma ya basu.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da ya kamata ka sani game da harin da yan bindiga suka kai NDA

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sojan da yan bindiga suka sace a NDA na nan da ransa, bai mutu ba: FIJ
Sojan da yan bindiga suka sace a NDA na nan da ransa, bai mutu ba: FIJ
Asali: UGC

Majiyar ta bayyana cewa:

"Duk lokacin da suka kira a waya, su kan ba Dantong wayar suyi magana, don a tabbatar da cewa yana raye."
"Yana nan da rai. Wannan ina iya tabbatarwa. Kawo ranar 10 na daren Talata, yana raye - duk da rahotannin dake cewar ya mutu."

Wata majiya a NDA ta bayyana cewa hukumar Soji bata ji dadin yadda labarai ke fita kan lamarin ba.

Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci N200m kudin fansa

Yan bindigan da suka kai hari makarantar horar da Sojojin Najeriya NDA dake garin Afaka a jihar Kaduna kuma sukayi awon gaba da jami'in Soja sun bukaci kudin fansa N200m.

A cewar FIJ, yan bindigan sun kira NDA domin tattauna maganar kudin fansa kafin su sake shi.

Kara karanta wannan

Yan bindigan da suka kai hari NDA sun bukaci N200m kudin fansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel