Ahmad Joda bai taba neman alfarma waje na ba, Shugaba Buhari

Ahmad Joda bai taba neman alfarma waje na ba, Shugaba Buhari

  • Buhari ya yabawa Alhaji Ahmad Joda bisa irin kokarin da ya yiwa Najeriya
  • Shugaban kasan ya ziyarci jihar Adamawa don gaisuwar ta'aziyya
  • Ya siffanta Ahmad Joda matsayin dattijon da bai taba neman alfarma wajensa ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya siffanta marigayi Ahmad Joda a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga Najeriya lokacin da yayi ayyukansu na gwamnati.

Buhari yace duk shekarun da ya san Joda, bai taba neman alfarma wajensa ba, rahoton DailyNigerian.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayinda ya kai ziyara fadar Lamidon Adamawa, Muhammadu Barkindo Mustapha, ziyarar ta'aziyya da ya kai kan mutuwar wasu shahrarrun yan jihar Yola.

Ahmad Joda bai taba neman alfarma waje na ba, Shugaba Buhari
Ahmad Joda bai taba neman alfarma waje na ba, Buhari Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Daurin auren Yusuf Buhari: Yemi Osinbajo ya dira garin Kano

Yace iyalan wadanda Buhari ya kaiwa gaisuwar ta'aziyya sune Alhaji Ahmad Joda, Dr Mahmoud Tukur, da Abdullahi Danburam Jada.

Buhari yace:

"Tun lokacin da ya zama gwamnan Arewa maso gabas karkashin Janar Obasanjo da kuma bayan haka, Joda na cikin wadanda suka taimakeni, har zuwa lokacin rasuwarsa."
"Ya taimakeni duk lokacin da na nemi taimakonsa a matsayin gwamna, Minista da kuma shugaban kasa kuma bai taba neman alfarma daga wajena ba, na kudi ko wani abu."

Shugaba Buhari ya dira birnin Yola

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Yola, jihar Adamawa a ranar Juma'a, 20 ga Agusta, domin gaisuwar ta'aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Ahmed Joda.

Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Najeriya lokacin mulkin Soja kuma mutum na farko da Buhari ya ba mukami bayan nasara a 2015 , Alhaji Ahmed Joda, ya mutu.

Ya rasu ne ranar Juma'a, 13 ga Agusta a Yola, babbar birnin jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Buhari ya tausawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna, ya ce zai taimaka musu

Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel