Martani ga Jega: Gwamnoni sun ce sam APC ba ta ba 'yan Najeriya kunya ba
- Kungiyar gwamnoni sun hada baki sun ce Jega bai kyauta ba wajen cewa sun gaza a mulkinsu
- Wannan na zuwa ne bayan da Farfesa Jega ya zargi PDP da APC cewa sun gaza cika burin 'yan Najeriya
- Gwamnonin sun ce, Jega ya yi magana ne irinta 'yan siyasa bai kuma nuna karimci irin na masana ba
Abuja - Kungiyar gwamnoni ta yi fatali da ikirarin Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban INEC, cewa manyan jam’iyyun APC da PDP a kasar nan sun gaza kuma sun kunyata ‘yan Najeriya.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan ta Dr Salihu Lukman, Daily Trust ta ruwaito.
A cewar Lukman, Jega ba shi da wata hujja da za ta goyi bayan maganarsa, jaridar Punch ta kara da cewa.

Kara karanta wannan
Sojojin hadaka sun ragargaji 'yan Boko Haram da ISWAP a Borno, sun hallaka wasu adadi

Asali: UGC
A cewarsa:
"Batutuwa daga Jega, ikirarin cewa PDP da APC duk daya ne kuma sun gaza cika bukatun 'yan Najeriya bai kamata a yi wasa da su ba."
Jega ya yi magana ne irinta 'yan siyasa ba ta kwararru ba
A cewarsa, tsohon shugaban INEC din bai tabbatar da zargin ba fiye da tunanin mutane.
Ya kara da cewa:
"Daga sauraro da karanta rubutun hirar, mutum zai fahimci cewa Jega yayi magana ne irinta dan siyasa a cikin hirar fiye da nuna zama kwararren masani.
"Kasancewarsa memba na Jam'iyyar Redemption Party (PRP), batunsa ya fi nuna goyon baya ga jam'iyyarsa ta PRP sabanin duk wani abin da ya zarga na manyan jam'iyyun."
PDP: Gwamnatin Buhari na amfani da EFCC wajen cin zalin 'yan adawarta na PDP
A wani labarin, Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da amfani da hukumomin tsaro don murkushewa da cin zalin ‘yan adawa, The Cable ta ruwaito.
A cikin wata sanarwa da Kola Ologbondiyan, kakakin PDP ya fitar a ranar Asabar 21 ga watan Agusta, ya ce jam’iyyar APC na amfani da hukumar EFCC don cin zarafin shugabannin PDP “a sabon yunkurin murkushewa da raunana samuwar adawa”.
Ologbondiyan ya ce jam’iyyar APC tana kai hare-hare kan masu maganan da ba sa tare da su don “tayar da yanayi na rashin bin tsarin dimokradiyya” a kasar kafin zaben shekarar 2023.
Asali: Legit.ng