Da duminsa: 'Yan majalisa sun tsige kakakin majalisar jihar Kebbi
- An tsige Honarabul Ismaila Abdulmummuni Kamba, kakakin majalisar jihar Kebbi da mataimakinsa, Muhammadu Buhari Aliyu daga kujerunsu
- An nada Muhammad Abubakar Lolo mai wakiltar yammacin Bagudo a matsayin sabon kakakin da kuma Mohammed Usman Zuru a matsayin mataimakinsa
- Sai da 'yan majalisar guda 20 cikin 24 suka amince da tsige su daga kujerun nasu kafin hakan ya tabbata
Birnin Kebbi, Kebbi - An tumbuke Honarabul Abdulmummuni Kamba, kakakin majalisar jihar Kebbi da mataimakinsa, Muhammadu Buhari Aliyu daga kujerunsu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, sai da 'yan majalisar 20 cikin 24 suka amince kafin a tsigesu daga madafun ikon nasu.
Yanzu haka an daura Muhammad Abubakar Lolo, dan majalisa mai wakiltar Bagudo ta yamma a matsayin kakakin majalisar, sannan Muhammad Usman Zuru mai wakiltar mazabar Zuru ya zama mataimakinsa.

Asali: Original
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng