Lady Adanma, matar Michael Okpara, tsohon firemiyan yankin gabas ta rasu

Lady Adanma, matar Michael Okpara, tsohon firemiyan yankin gabas ta rasu

  • Lady Adanma Okpara, matar marigayi tsohon firemiyan yankin gabas, ta riga mu gidan gaskiya
  • Ta rasu ne sa'o'in farko na ranar Litinin yayin da watanni kadan suka rage ta cika shekaru 97 a duniya
  • Ga wadanda suka san Lady Adanma, ana kwatanta ta da ginshikin nasarorin da mijinta ya samu yayin shugabancinsa

Abia - Gwamnatin jihar Abia ta bakin kwamishinan yada labarai da tsare-tsare, Chief Okiyi Kalu, ya tabbatar da mutuwar Lady Adanma Okpara, matar Michael I. Okpara, tsohon firemiyan yankin gabas na kasar nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Matar marigayi tsohon firemiyan ta rasu ne a sa'o'in farko na ranar Lahadi, 22 ga watan Augustan 2021.

Lady Adanma, matar Michael Okpara, tsohon firemiyan yankin gabas ta rasu
Lady Adanma, matar Michael Okpara, tsohon firemiyan yankin gabas ta rasu
Asali: Original

Za ta cika shekaru 97 a ranar 21 ga watan Disamban shekarar nan, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Wadanda suka san ta sun kwatanta Lady Adanma a matsayin ginshikin nasarorin da Dr. Michael I. Okpara ya samu a yayin shugabancinsa.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel