Magoya-baya suna zugo Ministan Buhari ya fito takarar Shugaban kasa a APC a 2023
- Kungiyar 'Senator Akpabio for Common Good' ta wanke Ministan Neja-Delta
- Ana zargin cewa tsoron hukumar EFCC ya sa Godswill Akpabio ya koma APC
- Wannan kungiya ta kare Ministan, tana nema masa goyon baya a zaben 2023
Abuja - Wata kungiyar siyasa mai suna Senator Akpabio for Common Good, ta na jan-kunnen ‘yan adawan tsohon gwamnan Akwa-Ibom, Godswill Akpabio.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa kungiyar Senator Akpabio for Common Good ta yi kira ga mau kokarin bata sunan Godswill Akpabio, su yi hattara.
A wani jawabi da shugaban kungiyar na kasa, Malam Jibril Tafida, ya fitar, ya yi kira ga Ministan harkar Neja-Deltan ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Da yake jawabi a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta, 2021, Malam Jibril Tafida yace ba a taba samun gwaninsu, Ministan da wani laifin rashin gaskiya ba.
Saboda EFCC Akpabio ya tsere daga PDP?
Rahoton yace kungiyar ta fitar da wannan jawabi a lokacin da ake rade-radin Ministan ya koma jam’iyyar APC ne domin gudun hukumar EFCC ta bincike shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tafida ya wanke Godswill Akpabio daga zargin da ake yi masa, yake cewa Ministan na Neja-Delta ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP ne domin ganin damansa.
Vanguard ta rahoto shugaban kungiyar magoya bayan yana cewa babu wanda ya tursasa wa Akpabio.
Kungiyar Senator Akpabio for Common Good ta kuma yi gargadi a kan jifan tsohon gwamnan da zargi da nufin a bata masa suna, duk da bautar da yake yi wa kasa.
A jawabin, Tafida yace bai kamata kuma a zargi Sanata Akpabio da hannu a binciken da EFCC ke kokarin yi kan tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson ba.
A cewar kungiyar, Ministan ya bar tarihi a lokacin da yake gwamna a Akwa Ibom, ganin yadda ya kawo gyara, ya inganta sha’anin ilmi, kiwon lafiya da wasanni.
A karshe ta yi kira ga mutane da kungiyoyi su mara wa Akpabio bayan zama shugaban kasa a 2023.
EFCC ta kyale gidan Kwankwaso
Rahotanni sun zo mana cewa jami’an EFCC sun yi maza, sun cire shingen da suka sa a daya daga cikin gidajen tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso.
Wani hadimin tsohon Ministan tsaro na kasar, ya shaida mana cewa EFCC ta goge tambarin da tayi a Amana House. A lokacin Sanata Kwankwaso ya na Abuja.
Asali: Legit.ng