Bayan ‘yan sa’o’i kadan, EFCC ta rabu da gidan Rabiu Kwankwaso da ta garkame a Kano

Bayan ‘yan sa’o’i kadan, EFCC ta rabu da gidan Rabiu Kwankwaso da ta garkame a Kano

  • EFCC sun cire lambar da su ka sa a wani ginin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • A makon da ya wuce, jami’an EFCC suka buga tambarin bincike a Amana House
  • Ba a dauki lokaci ba, sai aka ga hukumar EFCC ta rabu da gidan tsohon Gwamna

Kano - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta cire shingen da ta sa a ginin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa jami’an EFCC sun je, sun goge tambarin da suka yi wa gidan tsohon gwamnan Kano, na cewa ya na karkashin bincike.

A ranar Juma’a, 20 ga watan Agusta, 2021, hukumar EFCC ta rubuta ‘EFCC Keep Off' da 'EFCC under investigation' a jikin bango da kuma kofar shiga wannan gida.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hukumar EFCC ta rufe wasu dukiyoyin tsohon gwamna Kwankwaso a Kano

Daga baya sai aka ga an goge wannan rubutu da aka yi, EFCC ta rabu da gidan na Rabiu Musa Kwankwaso.

Da muka tuntubi wani daga cikin hadiman tsohon gwamnan na Kano, ya shaida mana cewa tun ranar Juma’a a cikin dare, jami’an EFCC suka cire shingen.

Jaridar Sahelian Times ta kawo labari cewa hukumar EFCC ta bambare takunkumin binciken da ta sa a kan kadarar tsohon Sanatan na yankin Kano ta tsakiya.

Gidan Rabiu Kwankwaso
Amana House Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Rahoton yace EFCC ta kyale gidan ne kusan kwanaki biyu bayan jami’an ta sun zo sun rufe shi.

Amana House

Wannan gini da ake kira Amana House, shi ne wanda tsohon Ministan tsaron ya damka wa gwamnati domin ayi jinyar wadanda suka kamu da COVID-19.

Wata majiya tace da farko jami’an hukumar sun garkame gidan ne a sakamakon wani korafi da aka kai.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta sako tsohon gwamna bayan damke shi da tayi da sa'o'i

Duk abin ke faruwa, Sanata Kwankwaso ba ya garin Kano. Washegarin ranar da abin ya faru, an gan shi a ta’aziyyar gidan Sanara Emmanuel Dangana a Abuja.

Oga 2023

A makon nan ne aka samu labari magoya-baya sun fito da hotunan neman takarar Shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Jama'a sun rika cin karo da hotunan Farfesa Osinbajo da Gwamna Ganduje a lokacin da suke hanyar zuwa garin Bichi wajen halartar bikin nadin sarauta da aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng