Dalilin da ya sa na cika da bakin ciki da nadama, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya magantu
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya waiwaya daga tun lokacin da Najeriya ke barin mulkin soja zuwa gwamnatin dimokuradiyya
- Atiku ya tuno farkon mulkin dimokuradiyya a Najeriya yayin da yake juyayin mutuwar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Nasiru Mantu
- Tsohon dan takarar shugaban kasar ya lura cewa marigayi tsohon dan majalisar yana daya daga cikin wadanda suka yi aiki don tabbatar da zaman lafiyar kasar a jamhuriya ta hudu
Mutuwar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ibrahim Nasiru Mantu, ya haifar da bakin ciki ga 'yan Najeriya da yawa, musamman ma daga bangarorin siyasa.
Daya daga cikin fitattun 'yan kasar da ya nuna tsananin dacin rai da bakin ciki shine Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, wanda ya kadu kan rasuwar Mantu, PM News ta ruwaito.
Atiku a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, ya tuna alakarsa da tsohon sanatan a lokacin da yake cikin rushasshiyar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) lokacin ya kasance babban ginshikin siyasa a babban Jam’iyyar Nigeria Republican Convention (NRC).
A cewar tsohon dan takarar shugaban kasar, Mantu ya yi aiki tare da wasu 'yan siyasa don daidaita dimokradiyya mai tasowa a farkon mulkin Jamhuriya ta hudu, Daily Nigerian ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Mantu ya kasance mai matuƙar mahimmanci a wajen gudanar da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a cikin waɗannan mawuyacin shekarun na koyon tsarin dimokuraɗiyya."
Ya nuna jajircewar Mantu a matsayin ɗaya daga cikin halayen da ba a saba gani ba waɗanda suka gina shi tun daga kasa har zuwa matsayin babban jigo.
Buhari ya yi alhinin mutuwar Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa
A gefe guda, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jajantawa iyalan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu, wanda ya rasu a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, yana da shekaru 74.
Punch ta ruwaito cewa mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 17 ga watan Austa.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Shugaba Buhari ya yi ta’aziyyar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu’.
Asali: Legit.ng