Mutum 50,000 a Sokoto sun yi gudun Hijra zuwa kasar Nijar sakamakon hare-haren yan bindiga

Mutum 50,000 a Sokoto sun yi gudun Hijra zuwa kasar Nijar sakamakon hare-haren yan bindiga

  • Dan majalisa a jihar Sokoto ya zargi gwamna Tambuwal da watsi da al'ummarsa
  • Hanarabul Boza yace sun kirga mutum 50,000 da sukayi gudun Hijra Nijar sakamakon matsalar tsaro
  • Matsalar tsaro ta zama babbar matsala a Arewa maso yammacin Najeriya

Sokoto - Sama da mutane 50,000 a garuruwa 17 dake karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto sun yi gudun Hijra zuwa jamhuriyyar Nijar sakamakon hare-haren yan bindiga.

Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltan mazabar Sabon Birni ta Arewa, Aminu AlMustapha Boza, ya bayyana hakan, rahoton DailyTrust.

Boza yace yanzu haka mutan wadannan kauyuka suna neman mafaka a kauyen Tudun Sunnah, dake karamar hukumar Gidan Runji, jihar Maradi a jamhuriyyar Nijar.

Dan majalisan ya kara da cewa ya dade yana kokarin ganin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, kan lamarin amma abin ya ci tura.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Kaduna kan raba kudin fansa, sun kashe juna har mutum 9

Yace:

"Na dade ina kokarin ganin gwamnan amma ya hana ni ganinsa saboda ya san dalilin da yasa nike son ganinsa."
"Ana kashe mutanenmu kullum. Kawo yanzu, mun kirga sama da mutum 50,000 da sukayi gudun Hijra jamhuriyyar Nijar. Sai da muka kwashe kwanaki biyu muna kidayarsu gaban gwamnan Maradi da shugaban karamar hukumar Gidan Runji."
"Na yi nadamar shiga siyasa. Na san irin gudunmuwar da muka baiwa gwamnan a karo na biyu saboda ya yi alkawarin bamu tsaro da cigaba, amma kalli mutanenmu yanzu, suna shan wahala kuma ko zuwa bai iya yi ko kuma ya turo wakilai ko akalla kayan tallafi."
"Lokacin karshe da ya zo garin shine lokacin da yan bindiga suka kashe mutane a Tarah bara."

Mutum 50,000 a Sokoto sun yi gudun Hijra zuwa kasar Nijar sakamakon hare-haren yan bindiga
Mutum 50,000 a Sokoto sun yi gudun Hijra zuwa kasar Nijar sakamakon hare-haren yan bindiga

Gwamna yayi martani

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Martani kan hakan, gwamnan Tambuwal ya musanta zargin cewa ya ki sauraron dan majalisar, ya ce ya kasance yana tuntubarsa kan lamarin tsaron yankin.

Mai magana da yawun Tambuwal yace gwamnan ya shirya zaman tsakanin kwamishanan yan sandan jihar, Dirakta na DSS a jihar da kuma dan majalisar inda aka fadawa dan majalisan cewa ya tuntubi mutum daya cikinsu idan akwai wata matsala.

Ya kara cewa an gayyaci dan majalisan zaman majalisar tsaro amma bai je ba.

Dan majalisan yace ba'a gayyace wata zaman majalisar tsaro ba

Amma dan majalisar ya karyata maganar cewa an gayyacesa wani zama na tsaro.

Yace kawai yayi magana da gwamnan ranar Alhamis da ta gabata inda yace masa ya kira Ministan lamuran yan sanda, Sanata Aliyu Wammako, Sanata Ibrahim Gibir da kuma shugaban hafsan Soji ya fada musu halin da al'ummarsa ke ciki.

Yace:

"Lokaci guda da ya kirani kenan kuma ga abinda ya fada min in yi."

Kara karanta wannan

Goggo: Gwamnatin Jihar Kano ta musanya rade-radin cewa ‘Murtala Garo zai gaji Ganduje a 2023’

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng