Shugaban kasar Afghanistan da ya sulale wa Sojojin Taliban, ya samu mafaka a Dubai

Shugaban kasar Afghanistan da ya sulale wa Sojojin Taliban, ya samu mafaka a Dubai

  • Kasar UAE ta tabbatar da cewa ta karbi Shugaba Ashraf Ghani da Iyalansa
  • Tsohon Shugaban kasar Afghanistan ya ruga Dubai bayan an karbe kasarsa
  • Ghani ya hau jirgi ya tsere bayan sojojin Taliban sun karbe ikon Afghanistan

United Arab Emirates - Gamayyar kasar Larabawa, ta ce ta karbi tsohon shugaban kasar Afghanistan, Ashraf Ghani, a sakamakon abin da yake faru wa.

Channels TV ta rahoto cewa Kasar United Arab Emirates ta bada sanarwa a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, 2021, cewa ta ba Ashraf Ghani da iyalinsa mafaka.

“Ma’aikatar kasar waje da ofishin huldar kasa-da-kasa ta UAE tana tabbatar da cewa ta na yi wa Ashraf Ghani da iyalinsa maraba da shigo wa kasar.”

Rahoton yake cewa kasar ta karbi tsohon shugaban na Afghanistan ne saboda jin kan Bil Adama.

Tabbatar da shigar Ashraf Ghani da iyalinsa UAE ya kawo karshen rade-radin da ake yi na cewa ya sulale ne zuwa Tajikistan, Uzbekistan ko Oman a ranar Lahadi.

Ghani mai shekara 72 a Duniya wanda ya zarce a kan mulki bayan zaben 2014, ya hakura da kujerarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasar Afghanistan
'Yan Taliban a ofishin shugaban Afghanistan Hoto: www.dw.com/en
Asali: UGC

Shugabanni suna samun mafaka a UAE

Jaridar tace ba wannan ne karon farko da wani shugaban Duniya ya fake a UAE ba. A 2017, tsohon firayim Ministan Thailand, Yingluck Shinawatra ya labe a Dubai.

Shi ma Sarkin Sifen Juan Carlos, ya samu mafaka a UAE a shekarar bara. A wannan kasa ne tsohuwar shugabar Fakistan, Benazir Bhutto ta yi shekara takwas.

Taliban sun karbe Afghanistan

The Cable ta ce Ghani ya tsere daga kasarsa ne a ranar Lahadi, 15 ga watan Agusta, 2021, a sakamakon cin karfin sojoji da kungiyar Taliban suka yi a Kabul.

Shugaba Ghani ya yi magana a shafinsa na Facebook, yake cewa ‘Taliban sun yi nasara’, ya tsere domin ya guje wa ‘zubar da jinin’ al’ummar kasar Afghanistan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel