Matasan Arewa suna so tsohon gwamnan Zamfara ya zama Shugaban APC, sun kawo dalilansu
- Concerned Citizens of Like Minds tana goyon bayan takarar Abdulaziz Yari
- Shugaban CCLM, Auwal D. Sani yace Yari ne ya dace ya zama Shugaban APC
- Tsohon gwamnan na Zamfara yana cikin masu neman shugabancin Jam’iyya
Yayin da ake cigaba da shirya wa zabukan shugabannin jam’iyyar APC, an samu wata kungiya da ke tare da tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari.
Yari ne ya dace - Concerned Citizens of Like Minds
Wata kungiya mai suna Concerned Citizens of Like Minds (CCLM), ta tsaida Alhaji Abdulaziz Yari a matsayin ‘dan takararta na shugaban APC na kasa.
Wannan kungiya ta Concerned Citizens of Like Minds ta ce babu wanda ya dace ya jagoranci jam’iyyar APC mai mulki illa tsohon gwamnan Zamfara.
CCLM tace Abdulaziz Yari yana da alaka da sauran jagororin jam’iyyar APC na fadin kasar nan, hakan zai taimaka wajen hada-kan duka ‘ya ‘yan jam’iyyar.
A cewar kungiyar Concerned Citizens of Like Minds ta gamayyar masu tunani, Yari zai kawo wa APC nasara idan har ya zama shugaban jam’iyyar na kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin da shugaban kungiyar ya fada
Daily Trust ta ce shugaban kungiyar, Auwal D. Sani, ya bayyana wannan a lokacin da ya tattauna da ‘yan jarida a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, 2021.
Jaridar ta rahoto Alhaji Auwal D. Sani yana cewa Yari ne ‘dan takarar da ya dace da wannan kujera.
“Mun yi imani cewa ‘dan takara daya ne yake da halayya da baiwa ta musamman wajen shugabanci da zai yi wa jam’iyyar APC abin da take bukata a yau."
Auwal D. Sani ya fada wa manema labarai cewa wannan ba kuwa ba kowa ba ne face Yari, wanda ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas a jihar Zamfara.
2023 ba dai da Secondus ba - Wike
Dazu ne aka samu labarin Nyesom Wike ya fito ya na cewa idan dai da gaske PDP tana so ta yaki jam'iyyar APC a zaben 2023, dole ayi waje da Prince Uche Secondus.
Gwamnan Ribas, Wike ya ce Uche Secondus ba zai iya jagorantar jam’iyyar PDP ta doke APC a 2023 ba. Wannan ya sa Wike ya dage a kan a ruguza majalisar NWC.
Asali: Legit.ng