Dan Najeriya Musa Mustapha ya zama zakaran dan wasan Tebir-Tenis na U-11 a duniya

Dan Najeriya Musa Mustapha ya zama zakaran dan wasan Tebir-Tenis na U-11 a duniya

  • Musa Mustapha ne namiji mai kasa da shekara 11 a duniya wanda yafi kwarewa a wasan Tebir
  • Mustapha yace ya fara buga wasan ne tun yana dan shekara 9
  • Ya ce ya yi mamakin labarin cewa shine zakaran dan wasa a duniya

Wani dan Najeriya mai shekaru 11 kacal da haihuwa, Musa Mustapha, ya zama zakaran dan wasan Tebir na yan kasa da shekara11 a duniya.

Yayin hirarsa da BBCNews Pigdin, dan yaron yace ya fara buga wasan Tebir-tenis ne tun yana dan shekara 9.

A cewarsa, har yanzu bai ga wani sauyi ba tun da ya zama zakaran duniya.

A cewarsa:

"Na fara buga wasan Tebir-Tenis tun ina dan shekara 9. Mahaifi na bai san ina bugawa ba. Amma wata rana yace mu rakashi inda ake bugawa kuma ya ga muna bugawa."

Kara karanta wannan

Har yanzu bamu kammala bincike kan Abba Kyari ba, Hukumar yan sanda

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sai ya sama mana mai horo wanda ya fara horar da mu. Da haka muka fara."

Abinda yasa yake jin dadin buga Tebir

Musa yace yana jin dadin buga wasan kuma yana kara masa karfin gwiwa. A cewarsa yana buga wasan kwallo, da sauransu.

Dan yaron yace bai jin dadi idan wani ya kadashi a wasan.

Yace yana son zaman zakaran wasan a duniya idan ya girma kuma zai so zama injiniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng