Babu maganar kara farashin man fetur daga N165 zuwa N300, gas zai rage tsada inji Minista

Babu maganar kara farashin man fetur daga N165 zuwa N300, gas zai rage tsada inji Minista

  • Gwamnatin Tarayya tace man fetur ba zai kara kudi a irin halin da ake ciki ba
  • Duk da an shigo da dokar PIB, ba za a bar farashin a hannun ‘yan kasuwa ba
  • Timipre Sylva yace za a rage tsadar gas a wani zama da zai yi da masu sana’ar

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bada sanarwar cewa farashin Premium Motor Spirit (PMS), abin da aka fi sani da man fetur a Najeriya, ba zai tashi sama ba.

Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, 2021, gwamnati ta ce za a cigaba da saida litar fetur a kan N162 zuwa N165.

Za a bi PIB sannu a hankali

Duk da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar PIB, wanda ta soke tallafin man fetur, litar mai ba zai kara tsada ba tukuna.

Kara karanta wannan

Farashin litar man fetur zai iya kai N300 bayan Shugaba Buhari ya sa hannu a dokar PIB

Sabuwar dokar PIB da ta shigo, ta ba ‘yan kasuwa damar tsaida farashin litar fetur a Najeriya.

Karamin Ministan harkar mai, Timipre Sylva, yace gwamnati ba za tayi saurin dabbaka wannan tsari ba, za ta bari a cigaba da saida fetur a tsohon farashi.

Timipre Sylva da yake bayani a jiya, yace idan aka bar mutane da ‘yan kasuwa, za a sha wahala, don haka abin da ya dace shi ne a bar farashi yadda ya ke.

Timipre Sylva
Ministan fetur, Timipre Sylva @HeTimipre Sylva
Asali: Twitter

“Babu wani karin farashi zuwa yanzu dai. Mun fara barin farashi a hannun ‘yan kasuwa. Za mu yi wannan a lokacin da mu ka yi tanadin da zai ragewa jama’a radadin tattalin arziki.”

Wace shawara Gwamnoni su ke kawo wa?

A cewar tsohon gwamnan, kungiyar gwamnoni na kasa tana ta kira a tashi farashin fetur domin ta haka ne kawai jihohi za su samu kudin aiwatar da ayyuka.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Game da 3% da aka ware wa jihohin da ake harko mai a karkashinsu, Sylva ya kare majalisa, yace idan har aka ware kason da ya zarce hakan, za a samu cikas.

“An yi la’akari da abubuwa da yawa kafin a tsaya a kan 3%. Domin kanmu gaba daya aka yi haka."
"Idan muka sa 10% a matsayin kason jihohin da ake hako mai a kasarsu, kamfanonin za su kara kudin kayansu, a karshe ‘yan kasa ne za su kare da tsadar.”

Har ila yau, Ministan ya bayyana niyyar gwamnatin tarayya na zama da masu kasuwancin gas domin ganin yadda za a samu rage farashi a fadin kasar nan.

Gwamnati na shirin cefanar da NNPC

An samu rahoto cewa NNPC zai tashi daga hannun gwamnatin tarayya, zai koma NNPC Limited a karkashin kulawar ma'aikatar kudi ta kasa, nan da watanni.

An dauki wannan mataki ne a sakamakon shigo da dokar nan ta PIB da aka yi a raanar Litinin.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel