Idan Abba Kyari ya san yana da gaskiya ya mika kansa hannun FBI kawai: Kaakin gamayyar kungiyoyin Arewa
- Daya daga cikin masu kare muradin Arewa yace a ra'ayinsa kawai Abba Kyari ya tafi Amurka
- A cewarsa, kin mikashi ba zai hana kotun Amurka cigaba da kararta ba
- Abdulaziz ya bayyana hakan ga wasu a sirrance amma bayanin ya fito
Kakakin gamayyar kungiyoyin Arewa CNG, AbdulAzeez Sulaiman, ya bayyana cewa a ra'ayinsa, idan Abba Kyari ya san yana da gaskiya ya mika kansa ga Amurka.
Wannan ya bayyana ne a faifan bidiyon da jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta na Youtube.
AbdulAzeez ya ce wannan ra'ayinsa ce ta kansa saboda bai kamata a rika kare mutum ba tare da wata hujja ba.
A jawabin da yayi, ya ce ya tabbata bai kamata ace Najeriya tace ba za'a bari an kaishi Amurka ba.
Idan yanada gaskiya, dokokin Amurka basu lalata kamar na Najeriya ba, idan yanada gaskiya zasu wankeshi kuma har ya shigar da su kotu, a cewarsa.
Hakazalika ya kara da cewa idan kuma ba shi da gaskiya, toh bai kamata a baiwa mara gaskiya hakkin kare rayukanmu ba.
Yace:
"A ra'ayina idan ya san yanada gaskiya, kawai ya tafi Amurka. Dokokinsu basu lalace kamar namu ba. Kuma idan an wankeshi, zai isa shigar dasu kotu ma."
"Amma muce ba zai tafi ba, gaskiya bai kamata ba. Amma idan yana da kashi a gindi, to bai kamata mutum mara gaskiya a mika masa hakkin kare rayukanmu ba.,... Idan ba ya tsoro kawai ya tafi."
Rashin zuwan Amurka ba zai hanasu gurfanar da shi ba
Sulaiman ya kara da cewa rashin mika shi ba zai hana gurfanar da Abba Kyari ba ko yana Amurka ko yana nan.
"Dukkan wadannan hayaniyan ba zai hana kotun Amurka cigaba da karar ba da kuma kama shi da laifi ko baya nan ba, kuma hakan zai fi muni ma. Zasu kwace dukiyoyinsa dake waje kuma su kamashi ko ya bar hukumar yansa."
Bai kamata a rika kare mutumin da ake tuhuma ba
Yace:
"Bai kamata al'umma su rika kareshi mutumin da ake tuhuma. Shi yasa mu gamayyar kungiyoyin Arewa mukayi yaki ba dan Kabilanci ba, don ganin cewa an hukunta Kanu da Igboho."
"Saboda haka bai kamata yanzu muce kada a mika shi (Abba Kyari) ba."
Saurari jawabin a nan:
Asali: Legit.ng