Mun kashe kimanin bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Ondo

Mun kashe kimanin bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Ondo

  • Minista Sadiya Farouq ta kai ziyara jihar Ondo don ganin yadda ake daukar bayanan dalibai
  • Hajiya Sadiya ta bayyana adadin daliban da ake ciyarwa a jihar yanzu
  • Tace gwamnati ta kashe bilyan 1.8 cikin shekaru uku a jihar kadai

Ondo - Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe kudi N1.8bn wajen ciyar daliban makarantun a jihar Ondo kadai cikin shekaru uku.

Ministar manajin annoba da jin dadin jama'a, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan lokacin taron daukar sunaye da hotunan dalibai a jiihar Ondo.

Ta bayyana cewa wannan abu da ake yi zai taimaka wajen ajiye bayanan dalibai da amfani da su.

Ta ce kawo yanzu akwai sunayen dalibai 108,842 a cikin runbun bayanan kuma ta lashi takobin ci gaba da hakan don tattara bayanan yaran da ake ciyarwa.

Ministar ta tabbatar da cewa kawo yanzu an kashe N1.8bn cikin shekaru uku da suka gabata don ciyar da dalibai a jihar Ondo karkashin shirin NHGSF, rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shirin na cigaba da tafiya. Zamu dawo Satumba da Oktoba domin daukar bayanan sabbin dalibai da zamu fara ciyarwa da kuma wadanda zasu kammala karatu. Saboda haka abune mai cigaba."

Mun kashe kimanin bilyan 2 wajen ciyar daliban firamare a Ondo
Mun kashe kimanin bilyan 2 wajen ciyar daliban firamare a jihar Ondo
Asali: Twitter

Mun fidda mutum milyan 10 daga cikin talauci a shekaru shida, Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta fidda sama da yan Najeriya milyan 10 daga cikin bakin talauci ta shirye-shiryen tallafi da jin kai ta NSIP, cewar Minista Sadiya Farouq.

Hajiya Sadiya Umar Farouq, wacce take rike da kujerar Ministar tattalin annoba da tallafi, ta sanar da hakan ne a taron lissafin adadin mutanen dake fama da talauci a kasashe masu tasowa.

A jawabin da mai magana da yawunta, Nneka Ikem Anibeze, ya saki kuma Legit.ng ta gani, ya ruwaito ta tana cewa:

"Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu nasarar karfafa mutum sama da milyan goma da kuma tsamosu daga talauci ta shirye-shiryen gwamnatin masu yawa, wanda ya hada da shirin tallafi na NSIP.

Kara karanta wannan

An sake ceto wata dalibar Chibok a jihar Borno, ta dawo da yara biyu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel