Kisan Gillan Musulmai a Jos: An Kashe Daliban Jami'ar UNIJOS 3 Wasu Sun Bata Bayan Kisan Matafiya a Jos
- An kashe ɗaliban jami'ar UNIJOS guda uku yayin da aka nemi wasu biyu aka rasa bayan kisan matafiya a Jos
- Shugaban kungiyar ɗalibai ta ƙasa NANS reshen Filato, Jeremiah Dalong, shine ya bayyana haka ranar Talata
- Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta Filato da hukumar jami'ar su agazawa ɗaliban da abinci
Plateau - Aƙalla dalibai uku na jami'ar tarayya dake Jos (UNIJOS) ake tsammanin sun rasa ransu yayin da wasu biyu suka bata, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne bayan kisan gillan da aka yiwa musulmai matafiya a kan hanyar Rukuba ranar Asabar.
Hakazalika rahoton ya bayyana cewa wasu ɗaliban jami'ar biyar suna gadon asibiti ana duba lafiyarsu a babban birnin jihar.

Asali: UGC
Suwa suka aikata haka ga ɗaliban?

Kara karanta wannan
Zamu Ceto Malamai da Daliban Kwalejin Bakura da Aka Sace, Matawalle Ya Yi Alkawari
Ana tsammanin dai lamarin da ya ritsa da ɗaliban yana da alaƙa da harin ɗaukar fansa bayan kisan matafiya fiye da 20 a Jos.
Shugabn ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) reshen jihar Filato, Kwamaret Jeremiah Dalong, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Jos ranar Talata.
Wane hali daliban UNIJOS ke ciki?
Dalonga ya yi kira ga gwamnatin Filato, gwamnatin tarayya da kuma shugabannin jami'ar da su gaggauta tura kayan abinci ɗakin kwanan dalibai.
Kwamaret Dalong yace:
"Tun bayan saka dokar hana fita na tsawon awanni 24 da gwamnatin Filato ta yi, ɗalibai sun tattaru a ɗakunan kwanna su babu inda suke iya zuwa."
"Ya kamata a ɗauki matakin kwashe su zuwa ga iyalansu domin suna cikin wani hali."
A cewarsa, dalibai biyun da suka bata, ba'a sake ganin su ba tun ranar da wannan rikicin ya faru.

Kara karanta wannan
Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamnan Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jiharsa
Ba zamu baru a tada rikicin addini ba
A wani labarin kuma Ba Zan Bari a Tada Zaune Tsaye Ba, Gwamna Filato Ya Yi Kakkausan Magana Bayan Kashe Musulmai a Jos
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace ba zai lamunci duk wani yunkuri na tada rikici a jiharsa ba ta hanyar yaɗa labaran ƙarya, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Aƙalla matafiya 22 aka kashe a wani hari da aka kai kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta rewa, jihar Filato.
Asali: Legit.ng