Da duminsa: Shugaban 'yan bindiga, Dogo-Gide, ya sako 'yammata 3 na makarantar Yauri

Da duminsa: Shugaban 'yan bindiga, Dogo-Gide, ya sako 'yammata 3 na makarantar Yauri

  • Dogo Gide, hatsabibin shugaban 'yan bindiga, ya sako dalibai uku daga 'yanmatan kwalejin tarayya ta Birnin Yauri
  • An sace yaran ne bayan samamen da miyagun 'yan bindiga suka kai kwalejin kusan watanni biyu da suka gabata
  • An sako daliban uku ne tare da wani malaminsu daya tare da wani bature bayan sasancin da aka yi da miyagun

Birnin Yauri, Kebbi -Shugaban 'yan bindiga, Dogo Gide, ya sako dalibai uku na kwalejin gwamnatin tarayya dake Birnin-yauri wadanda suka sace yayin wani samame da suka kai wata biyu da ta gabata.

Daliban da aka samu uku an sako su ne da yammacin Lahadi tare da wani malaminsu da kuma wani bature kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da duminsa: Shugaban 'yan bindiga, Dogo-Gide, ya sako 'yammata 3 na makarantar Yauri
Da duminsa: Shugaban 'yan bindiga, Dogo-Gide, ya sako 'yammata 3 na makarantar Yauri
Asali: Original

An sako wadanda aka yi garkuwa dasu ne bayan sasancin da aka yi tare da wasu masu ayyukan sirri.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Daily Trust ta tattaro cewa wadanda aka satan an kwashesu zuwa Minna a jihar Neja daga Kontagora, wani kauye dake karamar hukumar Mariga a jihar inda aka mika su.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel