Gwamnati ta shigo iyalan yan ta'addan ISIS 22 Najeriya daga Libya

Gwamnati ta shigo iyalan yan ta'addan ISIS 22 Najeriya daga Libya

  • Gwamnati ta ceto yan Najeriya 101 daga rikicin Libya
  • Daga cikinsu akwai iyalan tsaffin yan ta'addan ISIS dake kasar Libya
  • An tabbatar da dukkansu babu mai cutar Korona kafin bari su shigo Najeriya

Abuja - Gwamnatin tarayya ta shigo wasu yan Najeriya 101 daga kasar Libya, cikinsu akwai iyalan yan ta'addan ISIS 22 da aka kashe yayin yaki.

Wadannan mutane sun dira birnin tarayya Abuja ne ranar Juma'a, rahoton Punch.

Wannan na kunshe cikin jawabin da shugaban sashen labaran hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje NIDCOM, Abdur-Rahman Balogun, ya saki ranar Asabar.

Sun samu kyakkyawan tarba daga jami'an ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, NIDCOM, hukumar kiyaye yaduwar cututtuka, hukumar yakan muggan kwayoyi, hukumar agaji na gaggawa, hukumar DSS, hukumar shiga da fice da hukumar tashar jiragen ruwa.

Kara karanta wannan

An yi jana'izar Musulmai 25 da matasan Irigwe suka kashe a garin Jos yau Asabar

Wani sashen jawabin yace:

"Wadannan yan Najeriya sun hada da iyalan tsaffin yan ta'addan ISIS 22 da aka kashe a Libya tare da yaransu."
"Babu mai cutar Korona cikin dukkansu kuma sun dira daidai karfe 10:15 na dare a tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe Abuja, cikin jirgin Airforce C130."

Gwamnati ta shigo iyalan yan ta'addan ISIS 22 Najeriya daga Libya
Gwamnati ta shigo iyalan yan ta'addan ISIS 22 Najeriya daga Libya Hoto: NIDCOM
Asali: UGC

Zai yi wahala a karɓi tubabbun 'yan Boko Haram a cikin garuruwan mu – Shehun Borno

Shugabannin gargajiya da na addini a Borno sun ce zai yi wahala a sake karbar 'yan Boko Haram da suka tuba cikin garuruwa su.

Shugabannin sun bayyana fargaba kan yadda sojojin Najeriya za su raba tubabbun 'yan Boko Haram da tsattsauran ra'ayi a karkashin shirin su na Safe Corridor.

Abubakar El-Kanemi, Shehun Borno, ya ce wannan abu ne mai kyau, amma mutane za su ci gaba da kasancewa cikin fargaba na bala'in tashin hankalin da aka shafe shekaru 12 ana yi, musamman mazauna garuruwan da za a mayar da masu tayar da kayar bayan.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tabbatar da kisan mutum 22 a Jos, ana zargin matasan Irigwe suka kai hari

Asali: Legit.ng

Online view pixel