Uwargida ta yi yunkurin hallaka kanta don mijinta na kokarin kara aure, an kaita asibiti

Uwargida ta yi yunkurin hallaka kanta don mijinta na kokarin kara aure, an kaita asibiti

  • Saboda Kishi, wata mata ta yi yunkurin hallaka kanta
  • Matar ta yi wanka da man fetur kuma ta kunna ashana
  • Allah ya kiyaye bata mutu ba kuma an garzaya da ita asibiti

Hukumar yan sanda a jihar Jigawa tace wata uwargida mai suna, Maimuna Wadaji, na kwance a asibiti bayan yunkurin hallaka kanta a karamar hukumar Dutse ta jihar.

Kakakin hukumar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai NAN a Dutse.

Mr Shiisu matar yar garun Runguma, ta aikata hakan ranar 6 ga Agusta.

Ya yi bayanin cewa matar ta yi yunkurin kashe kanta ne bayan samun labarin cewa mijinta na kokarin yi mata kishiya.

Kaakin yan sandan ya kara da cewa, daga samun labarin suka garzaya wajen kuma suka kaita asibitin koyarwan jami'ar tarayya dake Dutse.

Uwargida ta yi yunkurin hallaka kanta don mijinta na kokarin kara aure, an kaita asibiti
Uwargida ta yi yunkurin hallaka kanta don mijinta na kokarin kara aure, an kaita asibiti Hoto
Asali: Twitter

Yace:

"A ranar Juma'a, misalin karfe 10:00, yan sanda sun samu labarin cewa wata Maimuna Wadaji, yar garin Rungumai a karamar hukumar Dutse, ta yi yunkurin kashe kanta, yayinda tayi wanka da fetur kuma ta bankawa kanta wuta."

"Daga baya da ta ji azaba ta fara iwun neman taimako kuma aka kaita asibitin koyarwan FUD domin jinya."

A cewarsa, za'a gurfanar da ita a kotu bayan an sallameta daga asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel