Gwamnonin Najeriya 6 da suka kammala karatun Digirinsu na uku

Gwamnonin Najeriya 6 da suka kammala karatun Digirinsu na uku

Duk da cewa kammala karatun digiri ba ka'ida bane na zama gwamna ko rike wani mukamin shugabanci ba, amma yana da muhimmanci ga ilmin jagorantan al'umma.

Ga jerin gwamnonin da sukayi karatun doktora kamar yadda TheNation:

1. Samuel Ortom (Jihar Benue)

- Ya yi karatun firamare a John's Primary School, Gboko da St. Catherine’s Primary School, Makurdi

- Ya yi karatun sakandare a Idah Secondary Commercial College, Idah a 1976 amma bai samu kammalawa ba saboda rashin kudi

- Ya yi Difloma a jami'ar ABU Zaria da jami'ar jihar Benue

- Ya yi Doktaransa a jami'ar Commonwealth a 2014

2. Abdullahi Ganduje(Jihar Kano )

- Ya yi digirin farko a jami'ar ABU Zaria a 1975

- Ya yi digiri na biyu a jami'ar Bayero Kano

- Ya koma jami'ar ABU Zaria ya sake digiri na biyu ilmin shugabanci

- Ya yi digiri na uku a jami'ar Ibadan a 1993

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Manyan Shugabannin PDP Na Kasa 7 Sun Yi Murabus

Gwamnonin Najeriya 6 da suka kammala karatun Digirinsu na uku
Gwamnonin Najeriya 6 da suka kammala karatun Digirinsu na uku Hoto: thenationonlineng
Asali: UGC

3. Benedict Ayade (Jami'ar Cross River)

- Ya yi digiri na farko a jami'ar Ibadan 1988

- Ya yi digiri na biyu a Microbiology a 1980 a Ibadan

- Ya sake digiri na biyu MBA a jami'ar Ambrose Ali, Ekpoma

- Ya yi digirin zama lauya a jami'ar jihar Delta

- Ya yi digiri na uku a Ibadan a 1994

4. Okezie Ikpeazu (Jihar Abia)

- Ya yi digiri na farko a jami'ar Maiduguri inda yayi Clinical Biochemistry

- Ya koma yayi digiri na uku a Biochemical Toxicology

- Ya yi digirinsa na uku a jami'ar Calabar yana dan shekara 30 a 1994

5. Kayode Fayemi (Jihar Ekiti)

- Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Legas

- Yayi digirinsa na biyu a jami'ar Ife

- Yayi digirinsa na uku a King’s College London

6. Babagana Zulum (Jihar Borno)

- Zulum yayi digirinsa na farko a jami'ar Maiduguri a ilmin Injiniyancin aikin noma

Kara karanta wannan

Gwamna Dave Umahi yayi ikirarin cewa Allah dan jam'iyyar APC ne

- Ya yi digirinsa na biyu a jami'ar Ibadan a 1998

- Ya yi digirinsa na uku a jami'ar Maiduguri a 2009

- Ya zama Farfesa a jami'ar Maiduguri a 2010

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng