Jerin sunaye: Kaduna, Jigawa, Kebbi da wasu jihohi 10 sun samu sabbin kwamishanonin yan sanda
FCT, Abuja - Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya bada umurnin nada sabbin kwamishanonin yan sanda na jihohi 13, da birnin tarayya Abuja.
Kakakin hukumar, Frank Mba, a jawabin da ya saki ta shafin hukumar ta Facebook ranar Juma'a, 6 ga agusta, ya yi bayanin cewa an yi wannan sauyi ne domin kawo inganci ga tsaro.
Frank Mba yace jihohin da aka nada sabbin kwamishanoni sune:
1. Jihar Niger , CP Monday Bala Kuryas
2. Jihar Kwara, CP Emienbo Tuesday Assayamo
3. Jihar Nasarawa, CP Soyemi Musbau Adesina
4. Jihar Taraba , CP Abimbola Shokoya
5. Jihar Benue, CP Akingbola Olatunji
6. FCT Abuja, CP Babaji Sunday
7. Jihar Kogi, CP Arungwa Nwazue Udo
8. Jihar Kaduna, CP Abdullahi Mudashiru
9. Jihar Jigawa, CP Aliyu Sale Tafida
10. Jihar Enugu, CP Abubakar Lawal
FBI: A karshe Abba Kyari ya bayyana a gaban kwamitin bincike na 'yan sanda, ya kare kansa daga tuhuma
11. Jihar Cross River, CP Alhassan Aminu
12. Jihar Bayelsa, CP Echeng Eworo Echeng
13. Jihar Kebbi, CP Musa Baba
Kakakin yan sandan ya ce sauran manyan jami'an yan sandan da aka sauya da wurin aiki sune:
CP Ndatsu Aliyu Mohammed, a tsohon kwamishanan Enugu wanda aka mayar yanzu kwamishanan sashen yaki da damfara FCID, Abuja
CP Sikiru Akande, tsohon kwamishanan Cross River wanda yanzu aka mayar dashi sashen ICT a hedkwata Abuja.
CP Bankole Lanre Sikiru: CP INTERPOL, FCID Lagos;
CP Augustine Arop mataimakin kwamandan makarantar yan sanda dake Jos.
Hukumar 'yan sanda ta bayyana irin matakin da za ta iya dauka kan Abba Kyari
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta bayyana cewa kora kai tsaye na daya daga cikin hukuncin da ka iya hawa kan mataimakin kwamishinan 'yan sanda (DCP), Abba Kyari, idan aka same shi da laifin da ake tuhumarsa da shi.
Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta dakatar da Kyari kwanan nan bayan da Amurka ta gabatar da zarginsa da hannu a zambar dala miliyan 1.1 da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushipuppi ya aikata.
A bangaren Kyari, ya karyata dukkan wasu tuhume-tuhumen da ake akansa.
Asali: Legit.ng