Yanzu-yanzu: Bayan shekaru 20, Lionel Messi zai bar kungiyar kwallon Barcelona

Yanzu-yanzu: Bayan shekaru 20, Lionel Messi zai bar kungiyar kwallon Barcelona

  • Bayan shekaru 20, zaman Messi a Barcelona ya zo karshe
  • Barcelona tace abin yayi mata takaici amma abin ya ci tura
  • Mutane da dama a fadin duniya sun tofa albartakun bakinsu

Labarin da shigo mana da duminsa na nuna cewa babban dan kwallon Argentina, Lionel Messi, zai bar kungiyar kwallom Barcelona, bayan shekaru 20 a kungiyar.

Kungiyar kwallon ta sanar da hakan a jawabin da ta saki a shafinta na Facebook ranar Alhamis.

Barcelona tace:

"Duk da cewa FC Barecelona da Lionel Messi sun yi yarjejeniya kuma an yi niyyar rattafa hannu kan sabon kwantiragi yau, wannan ba zai yiwu ba saboda dokokin kudi na LaLiga."
"Sakamakon haka, Messi ba zai cigaba da kwallo a F Barcelona ba."
"FC Barcelona na mika godiyarta ga dan kwallon bisa gudunmuwar da ya bada kuma tana masa fatan alheri a rayuwar kwallonsa nan gaba."

Messi ya kwashe shekaru 20 a Barcelona kuma buga wasanni 778 inda yaci kwallaye 672.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka Sojoji 24 a kasar Chadi

Bayan shekaru 20, Lionel Messi zai bar kungiyar kwallon Barcelona
Yanzu-yanzu: Bayan shekaru 20, Lionel Messi zai bar kungiyar kwallon Barcelona Hoto
Asali: Getty Images

Yan Najeriya sun tofa albartakun bakinsu

Lauwali Umar yace:

"Ina Yan Barca kufara kuka munayinka Messi kamana daidai bana zamuci jakkai"

Abubakar As-sadeeq yace:

"Yaje man city kawai ai har yanzu da sauran sa"

Maryam Yunus Muhammad yace:

"Yaxo kano pillers riba biyu yaci gurasA kuma yasha pop cola"

Zaharaddeen Ibrahim yace:

"Allah yaraka takigona"

Anas Muhammad

Muna masa godiya bisa irin gudummawar daya bama barca, amma kam mu Barca mukeyi koda messi ko babu messi

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: