2023: Jerin wurare 3 da APC ta gagara gudanar da zabukan shugabannin mazabun Jam’iyya

2023: Jerin wurare 3 da APC ta gagara gudanar da zabukan shugabannin mazabun Jam’iyya

  • Akwai wuraren da shugabannin jam’iyyar APC ba su iya shirya zabukan mazabu ba
  • Zaben kanshiloli da shugabannin kananan hukumomi suka sa aka ki yin zabe a Abuja
  • Shari’ar da ake yi a kotu su ka sa aka daga zabukan jam’iyyar a jihohin Bayelsa, Imo

Najeriya – The Cable ta ce zuwa yanzu jam’iyyar APC mai mulki ba ta gudanar da zaben shugabanni na mazabu a gundumomi ba saboda wasu dalilai.

Rahoton ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta shirya zabuka a jihohon Bayelsa, Imo da birnin Abuja ba.

Meyesa aka dage zabukan APC a Abuja?

Shugabannin jam’iyyar APC ba su shirya zaben shugabanni mazabu a birnin tarayya Abuja ba ne saboda zaben kananan hukumomi da za ayi a cikin Nuwamba.

“Ba za ayi zabukan shugabanni a birnin tarayya Abuja ba saboda jam’iyyar ba ta son ta kawo wani rikici saboda zabukan mazabu su na karaso wa.”

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Yadda Gwamna Buni da Minista su ka sabawa umarnin Mataimakin Shugaban kasa

“Duk wata hayaniya da za a samu zai iya jawo wa jam’iyyar cikas a zabuka masu zuwa.”

Babu zabe a jihar Bayelsa sai an gama shari’a

A jihar Bayelsa kuwa, an dakatar da zaben shugabannin mazabu na jam’iyyar APC ne saboda wani hukuncin da Alkalin kotun tarayya, Enekinimi Uzaka ya zartar.

Alkali mai shari’a Enekinimi Uzaka ya bukaci a daga zabukan APC har sai an gama shari’a a kotu. Za a koma babban kotun a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, 2021.

Jam’iyyar APC
Gangamin APC Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Yaushe jam'iyyar APC za ta samu shugabanni a Imo?

Jam’iyyar ta janye shirya zabukan shugabannin mazabu a jihar Imo a sakamakon karar da wani ‘danta ya shigar gaban babban kotun tarayya da ke garin Abuja.

Shugaban karamar hukumar Ideato ta kudu, Okey Anyikwa ya nemi a hana APC shirya zabuka a Imo saboda kotun daukaka kara ta kara wa shugabanninta wa’adi.

Sashe na 12 na doka da tsarin mulkin jam’iyyar APC sun bukaci a samu shugabanni a mazabu. Tun 2020 jam’iyyar APC ta ruguza shugabanninta a fadin kasar.

Kara karanta wannan

APC za ta kori wasu jiga-jiganta bayan an samu rigingimu, rabuwar kai a zabukan Jam’iyya

Zabukan mazabu sun raba kan manyan APC

Kun ji yadda shugaban APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni da Ministan shari'a, suka hada-kai, suka tuburewa Yemi Osinbajo bayan taron da ya jagoranta a Aso Villa.

An ki sauraron shawarar mataimakin shugaban kasa Osinbajo, an soma zaben shugabanni a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi tafiya zuwa kasar waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng