Shugaba Buhari ya yi jawabi a wajen taron hadin gwiwar Najeriya da kasar Faransa

Shugaba Buhari ya yi jawabi a wajen taron hadin gwiwar Najeriya da kasar Faransa

  • Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi a kasar Faransa a gaban ‘yan kasuwa da jami’an gwamnati
  • Buhari ya godewa gwamnatin Emmanuel Macron a kan gudumuwar da Faransa ta ke ba Najeriya
  • Shugaban Najeriyar ya dura filin saukan jirgin birnin Faris a ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba, 2021

Paris - Yayin da shugaban Najeriya yake birnin Faris, kasar Faransa, ya halarci taron da aka shirya domin kara dankon zumunci tsakanin kasarsa da Faransa.

Mai girma Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi na musamman a wajen wannan taro da hadin gwiwar kasar Faransa da Najeriya a babban birnin Faris.

Da yake jawabi a dazu, 10 ga watan Nuwamba, 2021, Muhammadu Buhari ya mika godiya a kan taimakon da sauran kasashen Duniya suke ba gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Jirgin Buhari ya isa kasar Faransa domin halartar taron zaman lafiya na Duniya

Kamar yadda Buhari Sallau ya wallafa hotunan wannan taro a shafin Facebook, Buhari ya hadu da shugaban kamfanin This Day, Nduka Obaigbena kafin a fara taron.

Buhari ya hadu da shugaban kamfanin BUA

Haka zalika shugaban kasar ya hadu da shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Rabiu da kuma wakilan Najeriya a tafkin Chadi, Ambasada Babagana Kingibe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi dazu da rana, shugaban kasa Buhari ya tabbatar da cewa zai ba kasar Faransa hadin-kai wajen kawo karshen ‘yan bindigan da suka addabi Najeriya.

Shugaba Buhari
Buhari yana jawabi a Faris Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Najeriya ta godewa Emmanuel Macron

Vanguard tace Muhammadu Buhari a madadin gwamnatin tarayya ya godewa Emmanuel Macron a kan hadin-kai da gudumuwan da yake ba kasarsa.

An rahoto Buhari yana cewa gwamnatin tarayya tayi kokarin farfado da tattalin arziki da gina abubuwan more rayuwa domin al'umma su ji dadin rayuwa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya ce zai kafa wani tarihin da ba a taba ba a Najeriya kafin ya bar ofis

Buhari Sallau yace bayan wannan taron, Mai girma Muhammadu Buhari ya halarci liyafa tare da shugaban kasar Faransa a fadarsa Elysee Palace da ke Faris.

Wajen wannan liyafa, Buhari yace ziyarar da Emmanuel Macron ya kawo birnin Abuja a shekarar 2018 ta fara yin tasiri a bangaren tsare iyakoki da kasuwanci.

A game da batun tsaro, Buhari yace kasar Faransa ta taimaka wajen kawo zaman lafiya a yankin tafkin Chadi ta hanyar yakar ‘yan ta’adda da akidar ta’addanci.

Buhari ya isa birnin Faris

An ji cewa Muhammadu Buhari ya sauka a filin jirgin birnin Faris domin halartar taron PPF.

Bayan ganawarsa da Emmanuel Macron, an ji cewa Buhari zai yi jawabi gaban shugabannin Duniya. Za a fara taron daga ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel