Ba sassauci na ke so ba: Mutumin da aka yanke wa ɗaurin shekaru 205 don kashe ƴan uwansa 5 ya faɗa wa kotu

Ba sassauci na ke so ba: Mutumin da aka yanke wa ɗaurin shekaru 205 don kashe ƴan uwansa 5 ya faɗa wa kotu

  • Wani mutum mai suna Stokes da kotu ta yanke wa ɗaurin shekaru 204 a gidan yari ya ce ba sassauci ya ke nema ba
  • A ranar 27 ga watan Afrilun 2020 ne Stokes ya bindige ƴan uwansa biyar har lahira ya kuma kira ƴan sanda da kansa
  • Wani abin mamaki shine Stokes kansa ya ce bai san dalilin da yasa ya aikata wannan mummunan abin ba

Milwaukee, Wisconsin - An yanke wa wani mutum ɗan Milwaukee hukuncin ɗaurin shekaru 205 a gidan yari saboda bindige ƴan uwansa 5 har lahira.

Mutumin bai kuma bayyana dalilin da yasa ya aikata hakan ba yana mai cewa yana zuciyarsa cike ta ke da ƙiyayya, The Punch ta ruwaito.

Mutumin da aka yanke wa ɗaurin shekaru 205 don kashe ƴan uwansa 5 ya faɗa wa kotu
Mutumin da aka yanke wa ɗaurin shekaru 205 don kashe ƴan uwansa 5 ya faɗa wa kotu. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Stokes, mai shekaru 44 ya ce ba zai iya bayyana dalilin da yasa ya kashe ƴan uwansa kamar yadda rahoton na The Punch ya bayyana.

Sunayen yan uwansa da ya kashe

Wadanda ya kashe sune Terese Thomas, mai shekaru 41, da yaranta biyu, Tiera mai shekaru 16 da Demetrius Thomas mai shekaru 14. Sauran yan uwansa sun hada da Marcus Stokes mai shekaru 19 da Lakeitha Stokes mai shekaru 17.

Jikan stokes mai shekaru uku ne kawai bai harbe ba. Masu bincike sun ce a gaban yaron abin ya faru amma ya roƙe shi ya ƙyalle shi.

Majiya daga jami'an tsaro ta ce Stokes ya kira ƴan sanda a 911 a ranar 27 ga watan Afrilun 2020, ya ce musu ya kashe iyalansa.

Alƙalin kotun Milwaukee, Mai Shari'a Michelle Havas ta yanke wa Stokes shekaru 40 a kan ko wanne kisan biyar.

Sannan ta ƙara masa shekaru biyar saboda mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba a matsayinsa na wanda aka taɓa samu da laifi a baya.

An Yanke Wa Jagoran Waɗanda Ke Sace Yaran Kano Su Sayar Da Su a Kudu Ɗaurin Shekaru 104 Tare Da Tarar Kuɗi

A wani labarin daban, babban kotun jihar Kano ta yanke wa Paul Owne, jagoran wadanda ke sace yaran Kano da sayar da su jihohin kudu hukuncin daurin shekaru 104 a gidan gyaran hali, Daily Trust ta ruwaito.

Kotun, wadda Mai shari'a Zuwaira Yusuf ke jagoranta ta yanke hukuncin ne a ranar Juma'a bayan wanda ake tuhumar ya amsa laifuka 38 da gwamnatin jihar ke zarginsa da aikatawa.

A cewar rahoton na Daily Trust, an gurfanar da shi ne bisa hada baki da wasu mutane shida domin sace wasu yara masu shekaru kasa da 10 a Kano kuma suka sayar da su a Onitsha, jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel